Gobara ta kone kamfanin giya na Najeriya a Aba

Gobara ta kone kamfanin giya na Najeriya a Aba

Wata wutar gobara da ta tashi ranar Juma'a ta kone wani sashe na kamfanin giyar Giuness dake garin Aba a jihar Anambra.

Jami'an hukumar kashe gobara sun sha matukar wahala kafin su iya shawo kan gobarar da ta fara ci tun karfe 11:00 na safiyar ranar juma'a har zuwa karfe 6:46 na yamma.

Okezie Uche, kwamanda hukumar kashe gobara, ya ce jami'an hukumar sa sun isa kamfanin na Guinnes da misalin karfe 1:00 na rana domin kashe gobarar tare da taimakon ma'aikata daga makobtan kamfanoni.

"Mun samu kalubale wajen samun ruwa, sai a NNPC muka samu ruwa.

"Bayan na ga wutar ta ki mutuwa ne sai na buga wayar shugaban hukumar kashe gobara na jihar Abia, Mista V. O Gbaruko, dake Umuahia domin neman agajin ma'aikata da kayan aiki.

Gobara ta kone kamfanin giya na Najeriya a Aba

Gobara ta kone kamfanin giya na Najeriya a Aba
Source: UGC

"Da taimakon sinadaran kashe gobara da NNPC ta bamu da dabarun ma'aikatun mu na kashe gobara mu ka samu damar shawo kan wutar.

"Ba don wadannan sinadarai da NNPC su ka bamu ba da ba lallai mu iya shawo kan gobarar ba," a cewar Uche.

DUBA WANNAN: Babban basaraken kabilar Igbo ya bawa Buhari gudumawar motar kamfen

Uche ya ce gobarar ta lalata kwalabe, robobin adana kwalabe, da kayayyaki da dama.

Ya kara da cewar, rashin alkinta kaya bisa tsari a bangaren ma'aikatan kamfanin ne silar tabarbarewar gobarar.

Wata majiyar 'yan sanda da ta nemi a boye sunanta ta ce sun samu labarin gobarar da misalin karfe 12 na ranar juma'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel