Babban basaraken kabilar Igbo ya bawa Buhari gudumawar motar kamfen

Babban basaraken kabilar Igbo ya bawa Buhari gudumawar motar kamfen

A yau, Asabar, ne mai martaba, Igwe Dennis Ezebuilo, wani sarki a Anambra ya bayar da kyautar wata mota kirar Toyota Hilux domin yakin neman zaben shugaba Buhari.

Da yake jawabi yayin bayar da motar a Abuja, Ezebuilo ya ce ya bayar da kyautar motar ne domin nuna godiya da farincikinsa bisa irin kokarin shugaba Buhari tun bayan shigar sa ofis a matsayin shugaban kasar Najeriya.

Wannan ba shine karo na farko da shugaba Buhari ya samu kyauta ko gudunmawar motar kamfen ba tun bayan fara yakin neman zabensa, sa dai wannan shine karo na farko da ya samu irin wannan kyauta daga wurin wanda ba dan siyasa ba kuma daga kudancin Najeria.

Ko a ranar Alhamis da ta gabata, sai da Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar sarkin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a yankin arewa maso gabas, Dakta Abiso Kabir, ya bayar da gudunmawar motoci domin tallafawa kamfen din Buhari da Farfesa Babagana Umara Zulum, dan takarar gwamnan jihar Borno.

Babban basaraken kabilar Igbo ya bawa Buhari gudumawar motar kamfen

Wasu motocin kamfen din Buhari
Source: Twitter

Da yake mika kyautar motocin ga gwamna Kashim Shettima na jihar Borno, Kabir ya yabawa gwamnan bisa zabo Farfesa Zulum a matsayin magajinsa, tare da bayyana cewar an yi abinda ya dace a lokaci da ya dace.

DUBA WANNAN: Jama'a sun cika makil a wurin taron kamfen din Buhari a Delta, hotuna

Ko a satin da ya gabata sai da Legit.ng ta kawo maku labarin cewar Jamilu Gwamna, Jigo a jam'iyyar APC kuma tsohon dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, ya bayar da kyautar wata zungureriyar mota a matsayin gudunmawar yakin neman zabe ga Buhari da dan takarar gwamna a jihar Gombe, Alhaji Yahaya Inuwa.

Da yake magana da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) bayan mika kyautar motar a Gombe, Gwamna ya ce Buhari da Inuwa na bukatar gudunmawa daga wurin 'yan Najeriya masu kishi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel