Wata jam'iyyar adawa ta goyi bayan takarar Buhari a zaben 2019

Wata jam'iyyar adawa ta goyi bayan takarar Buhari a zaben 2019

Jam'iyyar adawa a tarayyar Najeriya ta People’s Democratic Movement (PDM) ta bayyana cewa ta yi mubayi'a ga takarar tazarcen shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zaben da za'a gudanar nan da kasa da wata daya.

Shugaban jam'iyyar na kasa Sanata Abubakar Maadi shine ya bayyanawa shugaban kasar haka lokacin da ya kai masa ziyarar ban girma a ofishin sa ranar Juma'a kafin shiga masallaci.

Wata jam'iyyar adawa ta goyi bayan takarar Buhari a zaben 2019

Wata jam'iyyar adawa ta goyi bayan takarar Buhari a zaben 2019
Source: Twitter

KU KARANTA: An ce EFCC ta binciki surukin Buhari

Legit.ng Hausa ta samu cewa gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar ne ya jagorancin 'ya'yan jam'iyyar ta PDM zuwa wurin shugaban kasar jim kadan bayan sun gama tattaunawa.

Shi kuwa shugaban na People’s Democratic Movement (PDM), Sanata Abubakar, yayin ziyarar tasa ya kuma mikawa shugaban kasar wani kati dauke da sunaye da sa hannun dukkan shugabannin jam'iyyar ta su na amincewa da mubayi'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel