Jama'a sun cika makil a wurin taron kamfen din Buhari a Delta, hotuna

Jama'a sun cika makil a wurin taron kamfen din Buhari a Delta, hotuna

A yau, Alhamis, ne shugabannin APC, masoya da magoya bayan jam'iyyar da hadiman gwamnati suka hallara a jihar Delta domin yakin neman zaben shugaba Buhari a zaben shekarar nan da za a yi a watan Fabrairu mai zuwa.

An yi taron ne a garin Warri na jihar ta Delta, kuma ya samu halartar shugabanni da mambobin jam'iyyar APC daga fadin jihar da makobtan jihohi.

A jiya ne shugaba Buhari ya ziyarci jihar Kogi tare da kaddamar da yakin neman zabensa a jihar.

Jama'a sun cika makil a wurin taron kamfen din Buhari a Delta, hotuna

Kamfen din Buhari a Delta
Source: Facebook

Jama'a sun cika makil a wurin taron kamfen din Buhari a Delta, hotuna

Kamfen din Buhari a Delta
Source: Facebook

Jama'a sun cika makil a wurin taron kamfen din Buhari a Delta, hotuna

Yakin neman zaben Buhari a Delta
Source: Facebook

Jama'a sun cika makil a wurin taron kamfen din Buhari a Delta, hotuna

Buhari bayan ya sauka a Delta
Source: Facebook

A jiyan ne kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana da koshin lafiyar da zai iya sake mulkar Najeriya na tsawon wasu shekaru hudu.

Buhari ya ce ko jama'a zasu iya tabbatar da hakan daga yadda ake ganinsa a wuraren yakin neman zabe.

DUBA WANNAN: Zan canja gwamnan babban bankin kasa idan na ci zabe - Atiku

Buhari na wadannan kalamai ne yayin da ya bayyana tare da shi da mataimakinsa Osinbajo a wani shiri na kai tsaye da aka nuna a gidan talabijin na kasa (NTA).

Yayin shirin, Buhari da Osinbajo sun amsa tambayoyi daga jama'a a kan batutuwa da dama da suka shafi gwamnatinsu.

A shekarar 2017 ne shugaba Buhari ya shafe fiye da watanni uku yana zaman jinya a kasar Ingila, lamarin da yasa har yanzu wasu jama'a ke nuna shakku a kan batun koshin lafiyar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel