Hukumar NNPC ta samu dala miliyan 640.35 daga cinkin albarkatun man fetir

Hukumar NNPC ta samu dala miliyan 640.35 daga cinkin albarkatun man fetir

Hukumar man fetir ta Najeriya, NNPC, ta bayyana cewa ta samu makudan kudaden shiga daga cinikkayyar albarkatun man fetir a watan Oktoba na shekarar 2018 da suka kai dalan amurka miliyan dari shida da arba’in da dubu talatin da biyar (N$640.35).

Wadannan kudade sun tasan ma kimanin naira tiriliyan 2 da biliyan dari uku da hudu (N2.304trn), kamar yadda hukumar ta bayyana a ranar Laraba 16 ga watan Janairu yayin da take bayyana rahoton aikace aikacenta na wata wata.

KU KARANTA: Ana dara ga dare yayi: Ma’aikata sun fara yajin aiki a wannan jahar kwanaki 30 kafin zabe

A jawabin nata, NNPC tace kudin da aka samu a watan Oktoba ya haura wanda aka samu a watan Satumba, inda a Satumbar an samu dala miliyan dari biyar da shirin da bakwai da dubu saba’in ($527.70), hakan na nuna akwai cigaba mai kyau.

Hukumar NNPC ta samu dala miliyan 640.35 daga cinkin albarkatun man fetir

Hukumar NNPC
Source: UGC

A bayanin dalla dalla, hakikanin kudaden da aka samu daga sayar da man fetir da iskar gas sune dala miliyan 45.44, amma akwai yan canjin da aka samu daga kananan cinikayya da suka tasan ma dala miliyan 173.92 da dala miliyan 15.99.

Ita ma hukumar PPMC, wani reshe na NNPC ta bayyana cewa ta samu naira biliyan 231.33 daga sayar da fararen sinadarai a watan Otobar 2018, wanda hakan ya nuna cewar daga watan Oktobar 2017 zuwa Oktobar 2018 sun sayar da fararen sinadarai na naira tiriliyan 2.684.

“Domin tabbatar da an samu isashshsen man fetir a Najeriya ba tare da yayi karanci ba, an sayo litan mai guda biliyan 1.66, kwatankwacin litan a milyan 55.50 kenan a duk rana a watan Oktoba kadai.” Inji rahoton.

Sai dai rahoton ya bayyana damuwarsa NNPC game da karuwar fashe fashen bututun mai a duk fadin Najeriya, inda tace an samu karuwar fashe fashen butun mai da kashi 42.9 a watan Oktoba idan aka auna da wanda aka samu a watan Satumba.

A cewar rahoton an fasa bututun mai sau dari biyu da goma sha tara, 219, a watan Oktoba, kuma an fi samun matsalar fashe fashen a tsakanin garin Ibadan na jahar Oyo zuwa garin Ilorin na jahar Kwara, da kuma tsakanin garin Aba zuwa Enugu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel