Saurayi ya yiwa 'yan uwan sa Mata biyu fyade a jihar Legas

Saurayi ya yiwa 'yan uwan sa Mata biyu fyade a jihar Legas

Mun samu cewa kwazabar duniya ta sanya wani saurayi mai shekaru 19 a duniya, Andrew Chinedu, ya gurfana gaban Kuliya manta sabo ta Majistire da ke garin Ogudu sakamakon cin zarafi da keta haddin 'yan uwan sa Mata biyu.

Majiyar jaridar Legit.ng da ta kasance shafin jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Andrew ya gurfana gaban kotun ta Majistire sakamakon laifin da ya aikata na yiwa 'yan Mata biyu fyade ma su shekarun haihuwa na shida da takwas.

Saurayi ya yiwa 'yan uwan sa Mata biyu fyade a jihar Legas

Saurayi ya yiwa 'yan uwan sa Mata biyu fyade a jihar Legas
Source: Depositphotos

A bisa iko da kuma dama ta Alkaliyar kotun, Mai shari'a Misis E. Kubeinji, ta bayar da umarnin jefa Chinedu a gudan kaso inda zai bai wa dugadugan su hutu na tsawon kwanaki 65 gabanin sake waiwayar sa domin zartar da hukunci daidai da abinda ya aikata.

Jami'in dan sanda mai shigar da kara, Sufeto Lucky Ihiehie, ya bayar da shaidar yadda Chinedu ya aikata wannan muguwar ta'ada a tsakanin watan Yuni da kuma na Satumbar shekarar da ta gabata.

KARANTA KUMA: Ba bu ta yadda APC za ta ci ko da rumfar zabe daya a mazaba ta - Sanata Nwaoboshi

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Chinedu ya rika zakkewa kananan yaran karo bayan karo a a gida su da ke unguwar Irawo ta yankin Ikorodu yayin da mahaifan su ke gudanar da sabgogin gaban su na rayuwar yau da kullum.

Ihiehie ya ce wannan laifi ya sabawa sashe na 137 da kuma 259 cikin dokokin jihar Legas. Mai shari'a Kubienji, ta daga sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Maris na 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel