Zagon kasa: Okorocha da wasu mutane 6 na shirin fuskantar gwale-gwale daga jam'iyyar APC

Zagon kasa: Okorocha da wasu mutane 6 na shirin fuskantar gwale-gwale daga jam'iyyar APC

- Jam'iyyar APC reshen jihar Imo ta gayyaci gwamna Rochas Okoroha da wasu jiga-jigan jam'iyyar guda shida su gurfana gaban wata kwamitin ladabtarwa da aka kafa.

- Majiyar mu ta ruwaito cewa mutanen bakwai za su gurfana gaban kwamitin ne a ranar Laraba 16 ga watan Janairun 2019.

Wadanda aka gayyata sun hada da dan takarar sanata na Imo ta Gabas, Emma Ojinere; Dan takarar majalisar wakilai na tarayya mai wakiltan Ezinihitte Mbaise/Ahiazu Mbaise; Dan takarar majalisar wakilai na Ehime Mbano/IhitteUboma/Obowo, Rapheal Igbokwe.

Zagon kasa: Okorocha da wasu mutane 6 na shirin fuskantar gwale-gwale daga jam'iyyar APC

Zagon kasa: Okorocha da wasu mutane 6 na shirin fuskantar gwale-gwale daga jam'iyyar APC
Source: UGC

KU KARANTA: Jiga-jigan PDP 2 sun mutu a Arewa

Saura sun hada da mataimakin kakakin majalisar jihar Imo, Chike Okafor, da Ugonna Ozuruigbo da Eddy Iheancho da dan takarar gwamna, Obinna Mbata.

Kamar yadda ya ke a cikin wasikar gayyatar mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin, Matthew Omegara da sakataren kwamitin Kevin Ugwu, an gayyaci mutanen ne saboda laifukan yiwa jam'iyya zagon kasa.

Wasikar ta ce kwamitin zai dauki mataki a kan abin da ya kira 'munanan ayyukan' da suka aikata bayan kammala bincike.

Kwamitin za tayi zamanta a sakatariyar jam'iyyar da ke Owerri a ranakun 16 da 17 na watan Janairun 2019 daga karfe 9 na safiya zuwa 6 na yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel