Buhari da Osinbajo zasu halarci taron sauraron ra’ayin yan Najeriya da zai gudana a Abuja

Buhari da Osinbajo zasu halarci taron sauraron ra’ayin yan Najeriya da zai gudana a Abuja

A wani sabon salo da ba kasafai aka saba ganin haka ba, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo zasu halarci wani taro da zai gudana a babban birnin tarayya Abuja, inda zasu tattauna da yan Najeriya.

Za’a gudanar da wannan taro ne da misalin karfe 8 na daren Laraba 16 ga watan Janairu a dakin taro na Ladi Kwali dake otal din Sheraton, inda Buhari da Osinbajo zasu gana da yan Najeriya tare da sauraron ra’ayinsu na tsawon awanni biyu.

KU KARANTA: Yadda wani Dansanda direban bankaura ya bankade abokinsa Dansanda da mota

Buhari da Osinbajo zasu halarci taron sauraron ra’ayin yan Najeriya da zai gudana a Abuja
Buhari da Osinbajo
Source: UGC

Legit.ng ta ruwaito kaakakin yakin neman zaben shugaba Buhari, Festus Keyamo ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a daren Talata, inda yace zababbun mutane da aka gayyata ne kadai zasu samu shiga, kuma ana bukatar kowa ya isa dakin taron kafin karfe 7 na yamma.

Sai dai ga wadanda ba zasu samu damar halarta ko kuma ba’a gayyacesu ba, ana iya kallon shirin kai tsaye a tashashohin talabijin na Najeriya, musamman gidan talabijin na kasa, NTA.

Shi dai wannan sabon salon tattaunawa da gwamnatin Buhari ta bullo da shi, ta kirkiro shi ne domin baiwa Buhari da Osinbajo, yan takarkaru guda biyu dake neman zarcewa a mukamansu damar amsa korafe korafen yan Najeriya.

Shahararriyar yar jaridannan Kadaria Ahmed ce za ta jagoranci tattaunawar, kuma za’a nuna shirin kai tsaye a gidajen talabijin kamar haka TYC, Wazobia, Oat TV da dukkanin gidajen rediyo, har ma shafukan yana gizo za’a iya kallo don fadada rukunin mutanen da zasu iya aikawa da tambayoyinsu ga Buhari da Osinbajo.

An dade ba'a samu irin wannan dama da Buhari zai gana da yan Najeriya ba, tun farkon mulkinsa rabon da irin wannan ta samu, amma duba da bukatar siyasar 2019, zai gana da yan Najeriya kai tsaye.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel