Inyamurai za su fito su goyi bayan Buhari a zaben 2019 – Uzodinma

Inyamurai za su fito su goyi bayan Buhari a zaben 2019 – Uzodinma

- Sanata Hope Uzodinma yace Buhari zai mikawa mutanen Ibo mulki

- ‘Dan takarar na APC a Jihar Imo yace Inyamuri zai karbi mulki a 2023

- ‘Mai neman Gwamnan yace Ibo za su marawa APC baya a zaben bana

Inyamurai za su fito su goyi bayan Buhari a zaben 2019 – Uzodinma
Sanata Uzodinma yace Ibo zai karbi mulki da zarar Buhari ya gama
Asali: Depositphotos

Mun samu labari cewa Sanata Hope Uzodinma ya fito yayi ikirarin cewa lokaci ya kusa yi da Mutanen kabilar Ibo za su jagoranci kasar nan. Hope Uzodinma yayi wannan jawabi ne jiya Litinin a cikin garin Owerri a jihar Imo.

‘Dan takarar gwamnan na Imo a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ya bayyana cewa Mutanen Kudu maso Gabashin kasar nan sun shirya ba shugaba Buhari goyon baya a zaben da za ayi bana domin ganin ya samu nasara.

KU KARANTA: Sule Lamido, da Makarfi sun samu manyan mukamai a tafiyar Atiku

Sanatan ya kuma kara da cewa shugaba Buhari zai mikawa Ibo mulkin kasar nan ne da zarar wa’adin sa ya cika a shekarar 2023. Sanata Uzodinma yayi wannan jawabi ne lokacin kaddamar da manufofin takarar sa a jiya.

‘Dan takarar gwamnan na APC ya ce bayan ‘Yan Kudu sun taimaka wajen tazarcen Buhari a zaben da za ayi bana ne sannan APC za ta dauki mulki ta mika masu. Uzodinma yace Buhari ne kurum zai iya ba Ibo mulkin Najeriya.

A zaben 2015, shugaba Buhari ya samu kuri'u kasa da 200, 000 ne rak a yankin kudu maso gabashin kasar, a cewar sa dai ko a cikin wata karamar hukuma guda a Arewa zai iya samun wannan kuri'a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel