Ba mu gabatarwa Gwamnati wasu sababbin bukatu ba – Kungiyar ASUU

Ba mu gabatarwa Gwamnati wasu sababbin bukatu ba – Kungiyar ASUU

- ASUU ta nemi Gwamnatin Tarayya ta nuna za ta cika alkawarin da tayi

- Malaman Jami’ar sun ce yau za su sanar da jama’a game da yajin aikin

- Shugaban ASUU yace ba su neman wani sabon abu a hannun Gwamnati

Ba mu gabatarwa Gwamnati wasu sababbin bukatu ba – Kungiyar ASUU

ASUU tace Gwamnati ta saki wasu kudi ba ta so a tsaya a rubutu
Source: Depositphotos

Kungiyar ASUU ta malaman jami’an Najeriya tayi kira ga gwamnatin tarayya ta fito ta nuna tabbacin cewa a shirya ta ke da ta cika alkawarin da ta dauka kafin a janye yajin aikin da aka dauki dogon lokaci ana yi a fadin kasar.

Shugaban ASUU na kasa watau Biodun Ogunyemi, shi ne ya bayyana wannan a jiya Ranar Litinin a lokacin da yayi wata hira da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja, inda ya karyata cewa sun yi watsi da tayin gwamnati.

KU KARANTA: Matar Buhari tace wasu mutane 2 a PDP ne matsalar Najeriya

Farfesa Biodun Ogunyemi yake cewa labaran da wasu ke yadawa na cewa sun watsawa gwamnati kasa a ido, sam ba gaskiya bane, Ogunyemi yace ASUU ba ta mika wasu sababbin bukatu ko kuma tayi watsi da tayin da aka yi mata ba.

Shugaban na ASUU yace ba su ce dole gwamnati ta ta saki masu dukannin kudin da su ke bukata ba, sai dai su na nema ne a saki wasu daga cikin kaso na wannan kudi domin gyara makarantun gwamnatin da su ke naman lalacewa.

ASUU tace gwamnati tayi alkawarin biyan su alawus din su na kusan Naira biliyan 20 ba tare da bayyana lokacin da za a cika ragowar ba. A game da batun kudin jami’o’ kuma, ASUU ta nemi fara biyan na akalla shekara guda tukun.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel