Sule Lamido, Dogara, Ekweremadu da Makarfi sun samu manyan mukamai a tafiyar Atiku

Sule Lamido, Dogara, Ekweremadu da Makarfi sun samu manyan mukamai a tafiyar Atiku

- Jam'iyyar PDP ta yiwa wasu jiga-jigan 'ya'yanta nadin manyan mukamai domin samun nasarar dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar, Atiku Abubakar

- Wadanda aka yiwa nadin sun hada da Sule Lamido, Yakubu Dogara, Ike Ekweremadu, Sanata Ahmed Makarfi, Doyin Okupr da Alhaji Kawu Baraje

Jam'iyyar PDP ta nada wasu jiga-jigan 'ya'yanta hudu a matsayin masu bayar da shawara ga dan takarar shugaban kasar ta, Atiku Abubakar. Wadanda aka nada sun hada da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido; Kakakin Majalisar wakilai, Yakubu Dogara, Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da tsohon Shugaban jam'iyyar, Sanata Ahmed Makarfi.

Sule Lamido, Dogara, Ekweremadu da Makarfi sun samu manyan mukamai a tafiyar Atiku

Sule Lamido, Dogara, Ekweremadu da Makarfi sun samu manyan mukamai a tafiyar Atiku
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Nima ina fama da yunwa, Ministan Buhari ya fada a wurin kamfen

Har ila yau, jam'iyyar kuma ta nada Sule Lamido a matsayin shugaban kwamitin dattawa na yakin neman zaben Atiku. An kuma nada Alhaji Kawu Baraje a matsayin mai bayar da shawara ga Direkta Janar na yakin zabe, Sanata Bukola Saraki yayin da Doyin Okupe shi kuma aka nada shi mai bayar da shawara ga shugaban kamfen a fanin kafafen yada labarai.

Kazalika, Kungiyoyin 140 cikin 145 da suka janye goyon bayansu ga Atiku a baya sun sake dowawa jam'iyyar PDP bayan sunyi shafe wasu makonni tare da jam'iyyar APC.

Hadakan shugabanin kungiyoyin magoya bayan Atiku, ya ne ya sanar da dawowarsu a wani taron manema labarai da akayi a hedkwatan ofishin yakin neman dan takarar shugabancin kasar na PDP a yau Litinin a Abuja.

A kalla kungiyoyi 145 ne suka janye daga jam'iyyar ta PDP su koma goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari bisa zargin wariya da rashin kulawa da su da akeyi. Sai dai daga bisani sun ce sunyi sulhu da Shugaban kungiyoyin magoya bayan Atiku, Math Yeduna kuma yanzu sun dawo domin yiwa Atiku aiki.

Shugaban kungiyar, Mr Franklin Eze da skataren kungiyar na kasa, Oyegoke Olawole ya ce sunyi sulhu kuma ya nisanta kansu da wasu tsiraru da ke amfani da sunansu suna yiwa jam'iyyar APC aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel