2019: Jam’iyyu 61 na shirin maka Hukumar INEC a Kotu

2019: Jam’iyyu 61 na shirin maka Hukumar INEC a Kotu

Daily Trust ta rahoto cewa jam’iyyu sama da 60 su na shirin kai karar hukumar zabe na kasa watau INEC a gaban Kotun tarayya da ke Abuja. Jam’iyyun su na kukan cewa INEC ta na wasa da ka’idojin zaben kasar.

2019: Jam’iyyu 61 na shirin maka Hukumar INEC a Kotu

Jam'iyyun hamayya su na tunanin shigar da INEC Kotu
Source: Depositphotos

Jam’iyyu 61 ne su ke korafin cewa hukumar INEC ta taba ka’idojin zaben kasar da aka gindaya ta hanyar kawo wasu sababbin dokoki da ka iya sa a tafka murdiya a zaben da za ayi a shekarar bana kamar yadda mu ka samu labari.

Jam’iyyun sun nuna rashin yardar su da shirin da shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu yake yi. Jam’iyyun sun nuna cewa za su yi wa shugaban na hukumar INEC baran-baran idan har bai janye yunkurin na sa ba.

KU KARANTA: Yadda ‘yan siyasan Najeriya ke shirin murde babban zaben 2019

Shugabannin wadannan jam’iyyu na adawa sun nemi INEC ta guji fitar da sababbin dokokin zaben 2019 ba tare da tuntubar su ba. Ikenga Ugochinyere, wanda yake magana da yawun bakin sauran jam’iyyun 61 ne ya bayyana wannan a jiya.

Mista Ugochinyere yace dokar zabe da tsarin mulki sun ba su dama su kalubalanci sharudan zaben da INEC ta kafa a gaban Alkali idan har su na da wani ja. Ikenga Ugochinyere shi ne Sakataren kungiyar jam’iyyun nan na IPAC na kasar.

Sauran wadanda su ke kuka da shirin da INEC ta ke yi sun hada da: Shugaban APP Ikenga Ugochinyere; da shugaban GPN, Sam Eke; Nsehe Nseobong na jam’iyyar RP, Kenneth Udeze na jam'iyyar adawa ta AA.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel