Kuma dai! Makarantar sakandaren LAUTECH ta hana dalibai mata 55 shiga makaranta don sun sanya Hijabi

Kuma dai! Makarantar sakandaren LAUTECH ta hana dalibai mata 55 shiga makaranta don sun sanya Hijabi

Makarantar sakandaren dake karkashin jami'ar Ladoke Akintola dake garin Ogbomosho, jihar Oyo a ranan Litinin ta hana dalibai Musulmai mata 5 shiga makarantar saboda sun sanya Hijabi kan kayan makarantar.

Wani Malamin makarantar wanda aka sakaye sunansa ya bayyanawa manema labarai cewa an kori daliban ne yayinda sukayi kokarin shigowa harabar makarantar.

Malamin makarantar yace rikicin hana dalibai sanya Hijabi ya fara ne a shekarar 2011, lokacin da iyaye Musulmai suka mika bukatarsu ga makarantar cewa a halatawa yaransu mata masu niyyar sanya Hijabi sanyawa kan kayan makarantarsu bisa ga koyarwan addinin Musulunci.

Yace: "Tun shekarar 2011, an turawa shugabannin makarantar sakonni da dama kan wannan al'amari amma sukayi kunnen kashi. Yaranmu mata sun kasance suna amfani da hula sabanin Hijabi tun wannan shekarun, kuma haka ya sabawa koyarwan addinin Musulunci."

"Amma mukayi hakuri a matsayin yan kasa masu son zaman lafiya da kuma kyautata zaton cewa shugabancin makarantar zatayi adalci bisa ga kundin tsarin mulkin Najeriya kan yancin dan Adam."

"Bayan mun gaji da jira tun shekarar 2011, mun yanke shawara a ranan 4 ga watan Junairu, 2019 cewa daga ranan 7 ga wata, dalibanmu mata zasu fara sanya hijabi."

Amma shugaban makarantar, Ibrahim Animashahun, ya ce iyaye da dalibai suyi hakuri shugabannin makarantar su yanke shawara tukunna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel