Gurfanar da alkalin alkalai ta janyo cece-kuce a Najeriya

Gurfanar da alkalin alkalai ta janyo cece-kuce a Najeriya

Yan Najeriya kama daga shugabannin siyasa da na yankunan kudu, lauyoyi da sauransu sun yamutsa gashin baki akan yunkurin gurfanar da alkalin alkalai na kasar a aban kotun CCT kan zargin rashin bayyana gaskiyar kadarorin da ya mallaka.

Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta soki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tare da zargin ta da yunkurin rage wa bangaren shari’a karsashi a daidai lokacin da ke shirin gudanar da zaben 2019.

Hakan ya biyo bayan kotun da’a Ma’aikata ta bukaci alkalin alkalai, mai shari’a Walter Onnoghen da ya bayyana a gabanta a ranar Litinin, 14 ga watan Janairu domin amsa tambayoyi kan zargin da ake yi masa na cin hanci da rashawa.

A ranar Juma'a ne gwamnatin tarayya ta shigar da karar Onnoghen a gaban kotun da'ar ma'aikata bisa tuhuma guda 6 masu nasaba da bayyana kadarorin da ya mallaka.

Gurfanar da alkalin alkalai ta janyo cece-kuce a Najeriya

Gurfanar da alkalin alkalai ta janyo cece-kuce a Najeriya
Source: UGC

Dokar Najeriya ta bukaci manyan ma'aikatan gwamnati da su bayyana kadarorinsu gabanin hawa da kuma bayan sauka daga mukamansu.

Ana zargin Onnoghen da kin bayyana kudadensa a asusun da yake ajiyar Dalar Amurka da kuma wanda yake ajiye takardar kudin Pam na Ingila.

KU KARANTA KUMA: Sultan na Sokoto da sarakunan arewa sun gana don tattauna yadda za a bari yara mata su yi karatu (hotuna)

Tuni dai, wannan dambarwa ta dauki hankula matuka, in da gwamnonin yankin Kudu maso Kudancin Najeriya, suka bukaci Onnoghen da ya kaurace wa kotun ko kuma ya yi murabusa daga kujerarsa.

Sai dai wasu masana shari’a a Najeriya sun ce, babu wani mahaluki da ya fi karfin tuhuma a kasar muddin ana zargin sa da cin hanci da rashawa, illa shugaban kasa da mataimakinsa da kuma gwamna da mataimakinsa da ba za a tuhume su ba har sai bayan sun sauka daga mukamansu.

A halin da ake ciki, wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta dakatar da gwamnatin tarayya daga gurfanar da alkalin alkalai na kasa, Walter Onnoghen, a gaban kotun da'ar ma'aikata (CCT).

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel