Tafka tafkan jiragen ruwa guda 14 sun iso Najeriya dauke da kayan abinci

Tafka tafkan jiragen ruwa guda 14 sun iso Najeriya dauke da kayan abinci

Ba kasafai ake gane muhimmancin kayan amfani na yau da kullum ba har sai idan sun yi karanci a tsakanin jama’a, an nemisu an rasa, a wannan lokaci ne sai kaga duk arharsu a baya, sun kara kudi, kuma jama’a suyi ta rububin saye tunda dai babu makwafinsa.

Wasu daga cikin ire iren kayan masarufin nan sun hada da gishiri, siga, man fetir, kayan abinci da makamantansu, sai dai wani da yawa daga cikin ire iren kayannan shigo dasu ake yi daga kasashen ketare.

KU KARANTA; Gwamnatin Masari za ta fara kididdigan adadin mahaukata dake Katsina

Da wannan ne hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na Najeriya, NPA, ta sanar da shigowar wasu jiragen dankaro masu daukan mutum su dauki kayansa duk nauyinsu guda goma sha hudu zuwa Najeriya ta jahar Legas, a ranar Litinin 14 ga watan Janairu.

Jiragen sun rabu biyu ne, inda wasu suka sauka a tashar jirgin ruwa ta Apapa, yayin da wasu kuma suka sauka a tashar jirgin ruwa ta tsibirin Tin-Can, wasu daga ciki sun sauke man fetir da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.

Jirage guda uku daga ciki sun sauke man fetir ne da dangoginsa, yayin da sauran jirage goma sha daya suka sauke fulawa, kifi, gishiri, sundukai, man dizil, siga, man jirgin sama da sauran kayayyakin yan kasuwa.

Idan za’a tuna, ko a ranar Juma’a 11 ga watan Janairu, sai da wasu manya manyan jiragen ruwa guda Talatin da uku suka iso Najeriya, inda suka sauke kaya a tashashohin jiragen ruwa daga Apapa da na Tin Can a jahar Legas.

Hukumar NPA ce ta sanar da haka cikin wata sanarwa data fitar a Legas, inda tace jirage 21 daga ciki na dauke ne da man fetir, yayin da saura jirage 12 suke sauke siga, man jirgin sama, sundukai da fulawa, karafa da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel