Rashin hallaran Dino Melaye ya tsayar da shari’arsa

Rashin hallaran Dino Melaye ya tsayar da shari’arsa

- Hakan ya biyo bayan rashin hallaran sanatan wanda ayanzu yake tsare a hannun yan sanda tarayya da ke Maitama

-Hakan ya biyo bayan rashin hallaran sanatan wanda ayanzu yake tsare a hannun yan sanda

- Alkali ya dage zaman zuwa ranar 28 ga watan Janairu don ci gaba da sauraron shari’an

Shari’ar sanata mai wakiltan Kogi ta yamma, Dino Melaye ta hadu da cikas a ranar Litinin, 14 ga watan Janairu yayinda babbar kotun tarayya da ke Maitama ta ki ci gaba da sauraron shari’ar saboda rashin bayyanarsa.

Mista Melaye na fuskantar shari’a kan zargin bayar da bayanan karya ga al’umma game da wani yunkuri na kashe shi.

Rashin hallaran Dino Melaye ya tsayar da shari’arsa

Rashin hallaran Dino Melaye ya tsayar da shari’arsa
Source: UGC

Gwamnatin tarayya ta ofishin atoni janar na tarayya ce ta gurfanar da shi. An tsayar da ranar yau domin ci gaba da sauraron shari’ar.

A ranar Litinin, lauyan gwamnati, Shuaibu Labaran, ya fada ma kotu cewa sashin tsaro sun bukaci a dage zaman tunda Mista elaye na tsare har yanzu.

A nashi bangaren , lauyan wanda ake kara Olusegun Jolaawoz yayi bayani ga kotu kan dalilin da yasa akwai bukatar dage zaman.

KU KARANTA KUMA: Sultan na Sokoto da sarakunan arewa sun gana don tattauna yadda za a bari yara mata su yi karatu (hotuna)

Bayan sauraron bangarorin biyu, alkalin, Olasumbo Goodluck ya dage zaman zuwa ranar 28 ga watan Janairu don ci gaba da sauraron shari’an.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel