Yaki da ta’addanci: Janar Babangida ya jinjina ma Dakarun Sojojin Najeriya

Yaki da ta’addanci: Janar Babangida ya jinjina ma Dakarun Sojojin Najeriya

Tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya jinjina ma dakarun rundunar Sojojin Najeriya, wanda ya bayyanasu a matsayin gwarazan maza da suka ciri tuta, don haka sun cancanci yabo.

Legit.ng ta ruwaito IBB ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, 14, ga watan Janairu a garin Minna, babban birnin jahar Neja, don bikin ranar tunawa da yan mazan jiya, inda yace kokarin da suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya abin a yaba ne.

KU KARANTA: Gwamnatin Masari za ta fara kididdigan adadin mahaukata dake Katsina

Yaki da ta’addanci: Janar Babangida ya jinjina ma Dakarun Sojojin Najeriya

Dakarun Sojojin Najeriya
Source: UGC

A cewar IBB, Rundunar Sojin Najeriya ta yi namijin kokari wajen juya akalar yaki da ta’addanci, inda yace Sojojin sun cancanci yabo duba da yadda suka diran ma mayakan Boko Haram tare da karya lagonsu a yankin Arewa maso gabas.

“A duk shekara Sojojinmu suna buga kambun yabo da jinjina ga abokan aikinsu da suka kwanta dama ta hanyar gudanar da sha’ani daban daban har zuwa ranar 15 ga watan Janairu, a yayin da muke gab da fara shirin bikin bana, ina tunashemu da kada mu manta da cewa Sojojinmu na fuskantar babban kalubale.

“Kalubale na ta’addanci, da kuma kungiyoyin yan bindiga dadi, wannan kuma ya zama wajibi sakamakon kokarin da suke yi a yakin da suke yi da yan ta’adda da yan bindiga, kuma suna samu gagarumar nasara wajen kare martabar kasar.

“Amma ya zama wajibi nayi kira ga shuwagabannin Sojoji dasu samar da wasu sabbin dabarun yaki da zasu yi amfani dasu wajen kawo karshen yan ta’addan Arewa maso gabas gaba daya, daga karshe ina mika gaisuwa ga Sojojin da suka jikkata sakamakon yakin, tare da jinjin ga wadanda suka mutu a yakin.” Inji IBB.

Daga karshe IBB ya bayyana jin dadinsa da yadda Sojojin Najeriya ke gudanar da aikin samar da zaman lafiya a yankin kasashen Afirka da na majalisar dinkin duniya, don haka yayi kira gay an Najeriya dasu cigaba da basu goyon baya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel