Wata babbar kotu ta hana gurfanar da alkalai, ta jero dalilai

Wata babbar kotu ta hana gurfanar da alkalai, ta jero dalilai

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta dakatar da gwamnatin tarayya daga gurfanar da alkalin alkalai na kasa, Walter Onnoghen, a gaban kotun da'ar ma'aikata (CCT).

A ranar Juma'a ne gwamnatin tarayya ta shigar da karar Onnoghen a gaban kotun da'ar ma'aikata bisa tuhuma guda 6 masu nasaba da bayyana kadarorin da ya mallaka.

A yau, Litinin, ne kotun CCT ta bayyana cewar zata gurfanar da Onnoghen.

Sai dai bisa dogaro da wasu korafi guda biyu da aka gabatar a gaban kotun a yau, Jastis N. E Maha ya bukaci a dakatar da gurfanar da Onnoghen zuwa ranar 17 ga wata.

Wata babbar kotu ta hana gurfanar da alkalai, ta jero dalilai

Walter Onnoghen
Source: Facebook

Ya bayyana cewar a mika dukkan takardun biyu na korafi ga Onnoghen sannan ya bukaci dukkan bangarorin biyu (masy kara da wanda ake kara) su bayyana a gaban kotun ranar 17 ga wata.

An shigar da korafe-korafen ne a yau, Litinin, yayin da ake saka ran Onnoghen zai bayyana a gaban kotun CCT.

DUBA WANNAN: Ka daina yiwa Buhari sharri - Fadar shugaban kasa ta gargadi Ortom

Sai dai rashin bayyanar Onnoghen a gaban kotun CCT ya tilasta mata daga sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Janairu.

Sai dai hukuncin Jastis Maha na babbar kotun ta Abuja ya ce kar kotun CCT ta kara daukan wani mataki dangane karar Onnoghen har sai ranar 17 ga wata da zai saurari korafin biyu da aka shigar gabansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel