Nima ina fama da yunwa, Ministan Buhari ya fada a wurin kamfen

Nima ina fama da yunwa, Ministan Buhari ya fada a wurin kamfen

Direkta Janar na Kungiyar Yakin Neman Zaben Buhari, Rotimi Amaechi ya fadawa 'yan Najeriya da ke korafin cewa akwai yunwa a kasa cewa shima da kansa yana fama da yunwar.

Ya ce jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ne suka janyo yunwar a kasar ta hanyar sace kudaden da ke lalitar gwamnati a yayin da suke kan karagar mulki kamar yadda Punch ta ruwaito.

Amaechi ya yi wannan jawabin ne a wurin yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari da aka gudanar ranar Asabar a garin Bauchi.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya su fadawa PDP su dawo da kudaden gwamnati da suka sace.

Nima ina fama da yunwa, Ministan Buhari ya fada a wurin kamfen

Nima ina fama da yunwa, Ministan Buhari ya fada a wurin kamfen
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Legas: An kama manyan 'yan kasuwa dake daukar nauyin 'yan bindigar Zamfara

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya yi ikirarin cewa jam'iyyun adawar suna fama da talauci da yunwa a yanzu shi yasa suke kokarin ganin sun dawo kan mulki ko ta wane hali.

Ya ce, "Ina hira da wani abokina daga danyen bangaren sai ya ce min kana fama da yuna, sai na masa da ce, eh, idan da ba su sace kudaden kasa ba da yanzu kana cikin wadata.

"Kudin da suka sace ne ya jefa min yunwa. Ka fada musu, su dawo da kudaden.

"Jam'iyyar PDP ta ware $2 biliyan domin zaben shekarar 2015 amma duk da haka muka kayar da su. Sun talauce yanzu, yunwa na damunsu kuma suna son su dawo mulki su cigaba da sata.

"Idan sun ce ba bu abinci, suna son su dawo suyi sata ne amma ba za su iya hakan ba domin shugaban kasa ya ce kudin gwamnati ba na wasu tsirarun mutane bane."

Ministan sufurin ya ce bai san abinda PDP su kayi da kudaden da suka samu lokacin da ake sayar da ganganu mai a kan $114 na tsawon shekaru 16 ba.

Ya yi ikirarin cewa baya iya barci da idanu biyu a lokacin da PDP ke mulki a matsayinsa na gwamna saboda kallubalen tsaro da ake fama da shi a wannan lokacin.

Ya ce lamarin yanzu ya canja a karkashin gwamnatin Shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel