Ekweremadu ya bawa gwamnati shawara a kan gurfanar da alkalin alkalai na kasa

Ekweremadu ya bawa gwamnati shawara a kan gurfanar da alkalin alkalai na kasa

- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ik Ekweremadu ya ce tuhumar da ake yiwa alkalin alkalan Najeriya (CJN), Walter Onnoghen abu ne mai matukar hatsari ga demokradiyar Najeriya

- Ekweremadu ya ce matakin da gwamnati da dauka a kan alkalin alkalan yana iya raba kawunnan 'yan Najeriya tare da gabatar da Najeriya a matsayin kasar da ba ta biyaya ga doka a idanun duniya

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ik Ekweremadu ya yi kira ga Ministan Shari'a kuma Attorney Janar na tarayya ya yi gaggawar janye tuhume-tuhumen da ake yiwa alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen.

A yayin da ya ke tsokaci a kan gurfanar da alkalin alkalan na kasa a gaban kotun da'ar ma'aikata (CCT) bisa zarginsa da karya yayin bayyana kadarorinsa, Ekweremadu ya ce matakin da aka dauka a kan alkalin alkalan yana da matukar hatsari da demokradiyar Najeriya.

DUBA WANNAN: 2019: Ku zabi Buhari, kungiyar Izala ta umurci 'ya'yanta

A sakon da ya wallafa a shafukansa na kafafen sada zumunta na Twitter da Instagram a ranar Litinin 14 ga watan Janairu, ya ce matakin da aka dauka yana iya raba kan 'yan Najeriya tare gabatar da Najeriya a matsayin kasar da ba ta biyaya ga doka da kuma yiwa sashin shari'a katsalandan.

"Ina ganin tuhume-tuhumen da ake yiwa alkalin alkalan Najeriya, Justice Walter Onnoghen bai dace ba kuma yana da matukar hadari duba da cewa an yiwa shugaban majalisar Najeriya irin wannan tuhumar kuma ba a yi nasara ba," inji Ekweremadu.

"Wannan abu ne mai matukar hadari ga demokradiyar mu sai dai kawai ya raba kawunnan 'yan kasa tare da tsoma Najeriya cikin jerin kasashen da basu biyaya ga doka da kuma yiwa fanin shari'a katsalanda.

"Ina bawa Attorney Janar na Kasa shawarar ya janye wannan tuhume-tuhumen cikin gaggawa sannan ya bawa fanin shari'a hakuri. Ba zai yiwa mu cigaba a haka ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel