Dalilin da ya sa Buhari zai fadi zabe – Wani tsohon Gwamna Aliyu

Dalilin da ya sa Buhari zai fadi zabe – Wani tsohon Gwamna Aliyu

- Tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu, ya ce shugaban kasa Buhari zai fadi takara a zabe mai zuwa

- Yace manyan masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen nasarar zaben shugaban kasa a 2015 duk sun bar jam’iyyar mai mulki

- Aliyu yace jam’iyyarsa na sane da shirye-shiryen jam’iyya mai mulki na son yin magudin zabe, saboda ta rasa goyon bayan mutane

Wani tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fadi takara a zaben 2019..

Yace manyan masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen nasarar zaben shugaban kasa a 2015 duk sun bar jam’iyyar mai mulki.

Aliyu ya fadi hakan ne a wani hira da jaridar Punch a lokacin wani taron zaman lafiya wanda kwamitinsa ta yi da shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party reshen Plateau a garin Jos, babar birnin jihar a karshen mako.

Dalilin da ya sa Buhari zai fadi zabe – Tsohon Gwamna Aliyu

Dalilin da ya sa Buhari zai fadi zabe – Tsohon Gwamna Aliyu
Source: Facebook

Tsohon gwamnan yace jam’iyyarsa na sane da shirye-shiryen jam’iyya mai mulki na son yin magudin zabe, saboda ta rasa goyon bayan mutane.

Sannan yace PDP ma ta tanadi wani hanya na hana makircin yin magudi a zabe sannan zata tabbatar da cewa an kirga kuri’un mutane.

KU KARANTA KUMA: Yan iska sun kai hari yankin gidan iyalan Saraki, sun raunata mutum 11

A wani lamari na daban, mun ji cewa Sanata Ike Ekweremadu ya fito yayi maza yayi magana a kan jita-jitar da ake ji na cewa an samu sabani tsakanin kusoshin PDP a yayin da jam’iyyar ke dumfarar shiga babban zaben 2019.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar ya karyata cewa akwai wata baraka a PDP inda yace wasu ne kurum su ka saba shirga karya kuma har su kan jingina ta da shi. Ike Ekweremadu yace sam babu gaskiya a rade-radin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel