'Yan ta'addan PDP sun kai farmaki kan magoya bayan APC a Ilorin

'Yan ta'addan PDP sun kai farmaki kan magoya bayan APC a Ilorin

Za ku ji cewa adawar siyasa ta yi tsanani domin kuwa tarzoma a ranar Lahadin da ta gabata ta balle a jihar Kwara yayin da aka gwabza tsakanin magoya bayan manyan jam'iyyu na APC da kuma PDP.

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kwara na APC, Abdulrahman Abdulrazak, ya ce da kyar ya tsallake rijiya da baya yayin da ‘yan baranda na jam'iyyar PDP suka kai farmaki kan taron yakin neman zabe da aka gudanar a birnin Ilorin.

Ya ce gungun masu tayar da zaune tsaye na jam'iyyar adawa ta PDP, sun bude wuta ta harsashin bindiga kan al'umma yayin taron neman goyon baya da samun wurin shiga da jam'iyyar APC ta gudanar.

Hotun da Bidiyon yadda ta kasance kamar yadda dan takarar gwamnan jihar Kwara na APC, Abdulrahman Abdulrazak ya bayyana a shafin sa na zauren sada zumunta.

Dan takara Abdurahman yayin duban daya daga cikin wadan da tsautsayi ya afka ma su kwance a gadon asibiti

Dan takara Abdurahman yayin duban daya daga cikin wadan da tsautsayi ya afka ma su kwance a gadon asibiti
Source: UGC

Dan takara Abdurahman yayin duban daya daga cikin wadan da tsautsayi ya afka ma su kwance a gadon asibiti

Dan takara Abdurahman yayin duban daya daga cikin wadan da tsautsayi ya afka ma su kwance a gadon asibiti
Source: UGC

'Yan ta'addan PDP sun kai farmaki kan magoya bayan APC a Ilorin

'Yan ta'addan PDP sun kai farmaki kan magoya bayan APC a Ilorin
Source: UGC

Kimanin mutane biyu sun raunata tare da yiwa motoci da dama lahani yayin wannan abin Allah wadai da ya auku, inda dubunnan mutane suka nemi mafaka gami tserewa da kafufun su.

Hukumar ‘yan sanda ta Najeriya da sanadin kakakin ta na kasa, Jimoh Moshood, ya tabbatar da aukuwa wannan mummunan lamari na ta'ada.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Kwanaki 3 bayan rasuwar Sarkin Lafia, Marigayi Isa Agwa

Babban jami'I Moshood ya ce, ‘yan zafin kai na jam'iyyar PDP sun tayar kaya wajen kai farmaki tare da tarwatsa taron neman goyon baya da jam'iyyar APC ta gudanar a birnin Ilorin na jihar Kwara.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, wannan rahoto ya ci karo da ikirarin shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki da ya ce, mambobin jam'iyyar APC ke da alhakin kai farmaki kan ‘yan uwan sa da magoya baya a jihar Kwara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel