Hukumar yan sanda ta mayar da Melaye zuwa hedkwatar SARS

Hukumar yan sanda ta mayar da Melaye zuwa hedkwatar SARS

- Hukumar yan sanda ta mayar da Sanata mai wakiltan Kogi ta yamma, Dino Melaye zuwa hedkwatar sashin rundunar da ke kula da masu fashi da makami wato SARS a Guzape da ke Abuja

- An mayar da Dino hukumar SARS bayan yaki amincewa a kwantar da shi a asibitin DSS

- Yan sandan za su gurfanar da Melaye cikin kwanaki 14

Hukumar yan sanda ta mayar da Sanata mai wakiltan Kogi ta yamma, Dino Melaye zuwa hedkwatar sashin rundunar da ke kula da masu fashi da makami wato SARS a Guzape da ke Abuja.

Wannan shine karo da biyu da ake sauya wa sanatan wuri cikin kwanaki biyu kacal.

Da farko dai an mayar da sanatan zuwa asibitin hukumar yan sanda na farin kaya wato DSS a ranar Juma’a inda ya ci gaba da samun kulawar ma’aikatan jinya.

Hukumar yan sanda ta mayar da Melaye zuwa hedkwatar SARS

Hukumar yan sanda ta mayar da Melaye zuwa hedkwatar SARS
Source: UGC

Sakamakon kin shiga cikin asibitin DSS da ya yi, a jiya sai yan sandan suka yanke shawarar mayar da shi ga hedkwatar tawagar kwararru ta Intelligence Response Team (IRT).

Da yake tabbatar da sauya mashi waje, kakakin rundunar, Ag. DCP Jimoh Moshood, a jiya yace: “tawagar likitocn yan sanda na asibitinmu sun duba shi kuma sun tabbatar da cewa yana da lafiyar da zai iya tsayawa shari’a, amma ya nace kan cewa shi baida lafiya.

KU KARANTA KUMA: Wani mutum ya kashe matarsa da ‘ya’yansa 2 a Edo kan zargin kafirci

“Daga bisani sai muka dauke shi zuwa asibitin DSS a ranar Juma’a amma yaki shiga. Ya gwammaci ya kwana a waje. Nacewar da yayi kan cewa sai dai ya kwana a waje ya nuna cewa yana da lafiya.

“Don haka an kai shi don tsare shi a ofishin IRT sannan an bamu kwanaki 14 na tsare shi. Za a kai shi kotu a cikin kwanaki 14.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel