KAI TSAYE: Lauyoyi 94 sun dira CCT domin kare Alkalin alkalai, Walter Onnogehn

KAI TSAYE: Lauyoyi 94 sun dira CCT domin kare Alkalin alkalai, Walter Onnogehn

Legit.ng tana muku yadda abubuwa ke gudana da safen nan daga kotun CCT dake birnin tarayya Abuja inda ake shirin gurfanar da Alkalin alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen, bisa ga laifin mallakan wasu asusun bankin a kasashen waje.

Manyan Lauyoyi 94 karkashin jagorancin Wole Olanipekun sun dira zauren kotun CCT domin kare alkalin alkalai. Sauran lauyoyin sune tsohon ministan shari'a Kanu Agabi, Wole Olanipekun, Chief Chris Uche, Chief Adegboyega Awomolo da sauransu.

Mun kawo muku rahoton cewa Gwamnatin tarayya ta bukaci alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, ya yi murabus daga kujerarsa bisa ga zargin mallakan makudan kudade da yaki bayyanawa gwamnati.

A kan yunkurin tilastashi murabus, gwamnatin tarayya zata gurfanar da Jastis Walter Onnoghen, ranan Litinin, 14 ga watan Junairu gaban kotun CCT dake karkashin jagorancin Jastis Danladi Umar dake Abuja.

Jaridar PRNigeria ta bayyana cewa ta ga takardar karan da kotu ta aikawa alkalin alkalan ranan Juma'a a gidansa dake Abuja. Ana zarginsa da kin bayyana wasu dukoyoyi da ya mallaka kuma hakan ya sabawa dokar kasa ga ma'aikacin gwamnati.

Bugu da kari, ana zarginsa da mallakan wata asusun kudi cike da kudaden wajen irinsu Dala, Fam, da Yuro. Shima ya sabawa dokar kasa musamman masu rike da kujerara iko.

KALLI HOTUNAN:

KAI TSAYE: An shirya tsaf domin gurfanar da Alkalin alkalai, Walter Onnogehn

Kwandon abin zargi
Source: Original

KAI TSAYE: An shirya tsaf domin gurfanar da Alkalin alkalai, Walter Onnogehn

Lauyoyi na jira
Source: Original

KAI TSAYE: An shirya tsaf domin gurfanar da Alkalin alkalai, Walter Onnogehn

Lauyoyin gwamnati
Source: Original

KAI TSAYE: An shirya tsaf domin gurfanar da Alkalin alkalai, Walter Onnogehn

Lauyoyin CJN
Source: Original

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel