Kan kusoshin PDP a hada yake - Ekweremadu yayi watsi da rade-radi

Kan kusoshin PDP a hada yake - Ekweremadu yayi watsi da rade-radi

Mun ji cewa Sanata Ike Ekweremadu ya fito yayi maza yayi magana a kan jita-jitar da ake ji na cewa an samu sabani tsakanin kusoshin PDP a yayin da jam’iyyar ke dumfarar shiga babban zaben 2019.

Kan kusoshin PDP a hada yake - Ekweremadu yayi watsi da rade-radi

Ekweremadu yayi watsi da rade-radin cewa ya guji Atiku
Source: Facebook

Mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar ya karyata cewa akwai wata baraka a PDP inda yace wasu ne kurum su ka saba shirga karya kuma har su kan jingina ta da shi. Ike Ekweremadu yace sam babu gaskiya a rade-radin.

Sanata Ike Ekweremadu kara tabbatar da cewa kan PDP a hada yake gam, kuma a shirye su ke da su karbe mulki daga hannun jam’iyyar APC a zabe mai zuwa. Ekweremadu ya kara jadaddawa Duniya ce sam bai da niyyar barin PDP.

KU KARANTA: Ekwerenadu yayi watsi da yakin neman zaben Atiku Abubakar

Babban ‘dan majalisar yace tun lokacin da jam'iyyar PDP ta zama maras rinjaye a majalisa a 2015, ya bada tabbacin cewa babu abin da zai sa ya sauye-sheka. Sanatan yace sun sha wuya kafin jam’iyyar adawar ta dawo cikin hayyacin ta.

Ike Ekweremadu yace idan har bai bar jam’iyyar a wancan lokaci ba, ba zai taba yiwuwa ba kuma ya juyawa PDP baya a daidai wannan lokaci da ta ke gaf da siradin zaben 2019 inda su ke sa ran karbe mulkin kasar daga hannun APC.

Sanatan kasar duk yayi wannan jawabi ne a shafin sa na Facebook inda yace kwanan nan ya gana da Peter Obi da kuma gwamnonin Kudu karkashin jagorancin Dave Umahi domin ganin yadda Atiku da PDP za ta samu nasara a zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel