Masana sun nemi Gwamnatin Buhari ta daina biyan tallafin mai a Najeriya

Masana sun nemi Gwamnatin Buhari ta daina biyan tallafin mai a Najeriya

An fadawa gwamnatin tarayya cewa tayi amfani da wannan dama ta cire tallafin man fetur ganin yadda farashin man ya ruguje a kasuwannin Duniya. Manyan Masana sun ce yanzu ne ya fi dacewa da cire tallafin.

Masana sun nemi Gwamnatin Buhari ta daina biyan tallafin mai a Najeriya

Masana sun ce ya kamata a cire tallafin man fetur a yanzu
Source: Depositphotos

A daidai lokacin da ake saida gangar man fetur din Najeriya a kan kasa da $80 a kasuwannin kasar waje, wadanda su ka san harkar fetur sun nemi gwamnatin Najeriya ta cirewa kan ta daukar nauyin biyan tallafin man fetur

Daga cikin masu wannan kira akwai wata kwararriya a kamfanin DeltR Energy Ltd watau Ronke Onadeko. Misis Onadeko tace biyan cikon farashin mai bai da wani tasiri domin kuwa ‘yan kasuwa ne ke karkatar da kudin.

KU KARANTA: An bayyana abin da Gwamnatin Buhari ta ke kashewa kan tallafin fetur

Shugaban hukumar OGEES ta harkar man fetur a Jami’ar Afe Babalola, watau Farfesa Damilola S. Olawuyi ya goyi bayan haka, inda yace yanzu ne ya fi dacewa da gwamnati ta zare hannun ta daga biyan tallafin man fetur.

A halin yanzu darajar mai yayi kasa a Duniya don haka cire tallafin ba zai yi wa al’umma radadi sosai ba. Wannan ne zai sa masu adawa da tashin farashin man fetur a kasar su saduda a irin wannan lokaci inji Farfesa Olawuyi

Yanzu dai Najeriya na kashe makudan kudi kan tallafin fetur. Sai dai ana zargin cewa masu jigilar mai a kasar su na shiga da fetur kasashen ketare a boye su saida da tsada bayan sun karbi cikon kudin su a hannun gwamnatin tarayya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel