Zabe: Shugaba Buhari ya tarbi tsoffin Gwamnoni 2 da wasu mambobin PDP zuwa APC a wata jihar Arewa

Zabe: Shugaba Buhari ya tarbi tsoffin Gwamnoni 2 da wasu mambobin PDP zuwa APC a wata jihar Arewa

- Shugaban kasa Buhari ya tarbi wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

- Daga cikin wadanda su ka sauya shekar hardada tsoffin gwamnonin jihar Bauchi guda biyu, Ahmed Adamu Mu’azu da kuma Mallam Isa Yuguda

- Buhari, ya sha alwashin kwato dukiyar kasa daga hannayen barayin yan siyasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar Peoples Deocratic Party (PDP) mai adawa a kasar su goma sha takwas da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Daga cikin wadanda su ka sauya shekar hardada tsoffin gwamnonin jihar Bauchi guda biyu, Ahmed Adamu Mu’azu da kuma Mallam Isa Yuguda.

Zabe: Shugaba Buhari ya tarbi tsoffin Gwamnoni 2 da wasu mambobin PDP zuwa APC a wata jihar Arewa

Zabe: Shugaba Buhari ya tarbi tsoffin Gwamnoni 2 da wasu mambobin PDP zuwa APC a wata jihar Arewa
Source: Facebook

Buhari, ya sha alwashin kwato dukiyar kasa daga hannayen barayin da su ka sace ta, domin yin aiki ga ‘yan kasa, ya bayyana hakan ne a garin Bauchi, inda ya kai ziyarar wuni guda domin kaddamar da yakin neman zabensa a karo na biyu.

Sannan kuma ya kara jaddda kudurinsa na ci gaba da kare amanar da ‘yan kasa su ka ba shi.

KU KARANTA KUMA: Wani mutum ya kashe matarsa da ‘ya’yansa 2 a Edo kan zargin kafirci

Wasu ‘yan jam’iyyar ta su ta APC, sun bayyana cewa yanzu haka jam’iyyar ta zamo tungar mutanan da su ka wawure kudaden gwamnati, ganin yadda ake karbar masu canja sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa ta APC.

Wani dan siyasa ya ce daga hannun gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar, da Shugaba Buhari yayi tamkar yayi amaine ya lashe, domin kuwa ada can baya ya na shelar a zabi mutanan da su ka cancanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel