Yaki da rashawa: Idan rigima Buhari yake so, mu ma a shirye muke – Shugaban PDP Secondus

Yaki da rashawa: Idan rigima Buhari yake so, mu ma a shirye muke – Shugaban PDP Secondus

Shugaban jam’iyyar PDP, Cif Uche Secondus ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya kuskura ya jefa kasar Najeriya cikin tashin hankali, domin kuwa idan rigima yake so, suma a PDP sun shirya tsaf don bugawa da shi, inji rahoton Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Secondus ya bayyana haka ne dangane da badakalar Alkalin Alkalai Cif Walter Onnoghen da aka bankado cewa bai bayyana wasu makudan kudadensa kamar yadda doka ta ta tanada ba.

KU KARANTA: Mutuwar Sarkin Lafiya: Kalli wasu mutane 10 dake gwagwarmayar sun maye gurbinsa

Yaki da rashawa: Idan rigima Buhari yake so, muma a shirye muke – Shugaban PDP Secondus

Buhari da Shugaban PDP Secondus
Source: UGC

A yanzu haka ana sa ran gurfanar Alkalin Alkalan gaban kotun da’ar ma’aikata domin kaddamar da shari’arsa da za ta tabbatar da laifinsa ko kuma ta wankeshi daga tuhumar da ake yi masa, , wanda shine batun dake tayar da kura a farfajiyar siyasar Najeriya.

Shugaban PDP ya yi wannan jawabi ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Janairu a garin Jos na jahar Filato yayin gudanar da yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, inda ya bayyana haka a matsayin wata makarkashiyar magudin zabe da Buhari ke shiryawa.

A cewar Secondus, gwamnatin Buhari da jam’iyyar APC sun kaddamar da yaki da bangaren sharia ne ta yadda zasu samu damar gudanar da magudin zabe a zaben wata Feburairu na shekarar 2019, don haka suke kokarin cire Alkalin Alkalai.

“Kwanaki Talatin kafin zabe, amma Buhari da APC na kokarin kawo tashin hankali a Najeriya, ba zamu yarda da haka ba, idan har rigima suke nema, sun tareshi sun samu. Buhari da APC na kokarin tursasa ma bangaren sharia ne domin tayi musu biyayya, don haka dole ne yan Najeriya su yaki wannan yunkuri.” Inji shi.

Secondus yace idon Buhari ya rufe da neman mulki, shi yasa yake son ganin ya halaka shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki, sa’annan ya kama babban Sanatan adawa Dino Melaye.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel