Duniya juyi juyi: Tsofaffin shuwagabannin PDP 7 da suka sauya sheka zuwa APC

Duniya juyi juyi: Tsofaffin shuwagabannin PDP 7 da suka sauya sheka zuwa APC

Tun bayan taka kafarsa cikin farfajiyar siyasar Najeriya a shekarar 2003, Muhammadu Buhari ya yi tarayya da abokan siyasa iri iri daban, haka zalika ya hadu da abokan hamayya daban daban, wanda hakan yasa ya zamto tamkar maganan da ake cewa ‘Wani dare ne jemage bai gani ba?”0

Sai dai a yayin siyasar daga shekarar 2003 zuwa yanzu, Buhari yaci karo da abubuwan ban mamaki da dama, inda ya ga masoyinsa ya zama abokin hamayyarsa dare daya, sa’annan ya ga abokin hamayyarsa ya zama masoyinsa dare daya.

KU KARANTA: Mutuwar Sarkin Lafiya: Kalli wasu mutane 10 dake gwagwarmayar sun maye gurbinsa

Duniya juyi juyi: Tsofaffin shuwagabannin PDP 7 da suka sauya sheka zuwa APC

Tsofaffin shuwagabannin PDP 7 da suka sauya sheka zuwa APC
Source: UGC

Amma dayake burin duk wani dan siyasa shine samun karuwar magoya baya koda da mutum daya ne kuwa, don haka zamu yi duba ga wasu jigogin jam’iyyar PDP da suka sauya sheka suka dawo goyon bayan Buhari, duk da cewa bai taba yin PDP ba.

Majiyar Legit.ng ta bankado sunayen wasu tsofaffin shuwagabannin jam’iyyar PDP ta kasa da suka jefar da kwallon mangwaro domin su huta da kuda suka koma jam’iyyar APC da suka hada da;

- Audu Ogbeh

- Jim Nwodo

- Barnabas Gemade

- Vincent Ogbulafor

- Bamanga Tukur

- Adamu Muazu

- Ali Modu Sheriff

Duka gagga gaggan yan siyasan nan sun shuwagabanci jam’iyyar PDP a matakin kasa daga zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo har zuwa zamanin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma a yanzu dukkaninsu sun koma jam’iyyar APC.

Da wannan za’a iya tabbatar da batun da yan siyasa ke yin a cewa wai ba’a makiyi na dindindin kuma ba’a masoyi na dindindin a siyasa, don haka bai kamata mutum ya dinga zakewa a soyayya ko hamayyar siyasa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel