Yanzu Yanzu: Tsoro a Borno yayinda Boko Haram suka kai hari Magumeri

Yanzu Yanzu: Tsoro a Borno yayinda Boko Haram suka kai hari Magumeri

Ba a san adadin mutanen da suka mutu ba yayinda wasu yan bindiga da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari garin Magumeri, hedkwatar karaar hukuma a jihar Borno.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa yan ta’addan sun kai hari garin da misalin karfe 6 na yammacin ranar Lahadi, 13 ga watan Janairu.

An fara kai hari garin ne a ranar 25 ga watan Nuwamba, 2017, inda a lokacin aka kashe sojoji uku yayinda wasu shida suka ji rauni.

Ana nan ana tattara rahoton harin a daidai lokacin rubuto wannan rahoton amma wannan ba shine karo na farko da yan Boko Haram ke kai hari garin ba.

Yanzu Yanzu: Tsoro a Borno yayinda Boko Haram suka kai hari Magumeri

Yanzu Yanzu: Tsoro a Borno yayinda Boko Haram suka kai hari Magumeri
Source: Twitter

Rundunar sojin Najeriya sun daura alhakin harin Nuwamban 2017 akan hade kai da mazauna yankin suka yi da yan ta’addan; argi da shugabannin garin suka yi watsi da shi.

KU KARANTA KUMA: Tsoro na shi ne a ce Jam’iyyar PDP ta sake murde zaben bana – Darektan BCO

A baya mun ji cewa, a ranar Lahadi, da misalin karfe 1:00 na rana, kwararrun jami'ai na musamman suka yi nasarar gano wa tare da kwance wasu manya-manyan bamabamai da mayakan kungiyar Boko Haram suka binne a gefen titi.

Jami'an sun gano bamabaman ne ta hanyar amfani da na'ura yayin da suke gudanar da wani sintiri a kan hanyar Konduga zuwa Aulari a jihar Borno, kamar yadda rundunar sojin ta sanar a shafinta na Tuwita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel