Tsoro na shi ne a ce Jam’iyyar PDP ta sake murde zaben bana – Darektan BCO

Tsoro na shi ne a ce Jam’iyyar PDP ta sake murde zaben bana – Darektan BCO

Ministan sufurin Najeriya wanda kuma shi ne Darekta Janar na kungiyar nan ta Buhari Campaign Organisation, BCO, mai yakin ganin cewa shugaba Buhari ya zarce watau Rotimi Amaechi yayi wata hira da ‘yan jarida kwanan nan.

Tsoro na shi ne a ce Jam’iyyar PDP ta sake murde zaben bana – Darektan BCO

Rotimi Amaechi yace yana gudun Jam’iyyar PDP ta murde zaben 2019
Source: Depositphotos

A wannan hira, Ministan ya bayyanawa jaridar Daily Trust abubuwan da yake tunani za su faru a zaben da za ayi a shekarar nan tare da kuma irin shirin da su ke yi wajen ganin shugaba Buhari ya zarce a kan ragamar mulkin Najeriya.

Rotimi Amaechi ya fara da maidawa PDP martani na cewa APC ta jefa jama’a cikin yunwa, wanda a cewar sa gwamnatin baya ta jawo wannan matsala. Amaechi yace PDP ce ta sace dukiyar kasar wanda hakan ya jawo raunin tattali.

Ministan yace a sakamakon rashin kudi a kasar ne aka gaza samawa jama’a da dama aikin yi, wanda hakan kuma ya kawo yunwa da ake kuka. Ministan sufurin ya kuma koka da yadda farashin gangar mai ya ruguje a shekarun nan.

KU KARANTA: Tsohon hadimin Tinubu ya zama sabon kwamishinan 'yan sanda a Legas

Tsohon gwamnan ya nuna cewa duk da haka gwamnatin tarayya tana bakin kokarin ta a yanzu, domin a cewar sa babu inda Buhari ba ya aikin hanyoyi ko kuma dogon jirgin kasa domin cika alkawuran da APC ta dauka a zaben 2015.

Amaechi ya kuma nuna cewa zaben bana zai sha ban-ban da zaben 2015 domin kuwa a cewar sa, a wancan karo jam’iyyar PDP ta murde zaben da aka yi, inda yace a wannan karo kuwa, shugaba Buhari ba zai bari ayi magudi a Najeriya ba.

KU KARANTA: Osinbajo ya bayyana yadda PDP ta rika satar kudin al'umma a baya

Ministan yace abin da yake tsoron a zaben da za ayi shi ne jam’iyyar PDP ta murde zaben kasar. Ya kuma nuna cewa APC ta fi PDP yawon kamfe domin kuwa sun leka jihohi akalla 4 a cikin makonni 4 kacal da fara yawon yakin zabe.

Rotimi Amaechi yace matsalar da su ke samu ita ce rashin kudi, inda yace idan da yau za su samu kamar Naira Biliyan 2, da APC ta fita yawon kamfe. Ministan yace shugaba Buhari ya hana a dauki dukiyar kasa domin ayi kamfe da ita.

A bangaren tsaro ma dai Ministan ya nuna cewa yanzu abubuwa sun canza domin ‘yan ta’addan Boko Haram ba su iya kai hari kan jami’an tsaro kamar yadda aka rika yi a baya lokacin Goodluck Jonathan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel