Da dumin sa: Atiku Abubakar ya rasa magoya baya sama da 800,000 kudancin Najeriya

Da dumin sa: Atiku Abubakar ya rasa magoya baya sama da 800,000 kudancin Najeriya

Kwamiti na musamman dake rajin tattarawa da kuma wayar da kai al'umma don ganin an sake zabar shugaba Buhari a zaben 2019 mai zuwa watau Committee of Youth on Mobilisation and Sensitisation (CYMS) a turance sun ce sun karbi mutane daga tafiyar Atiku zuwa ta Buhari.

Kwamitin na matasa a ta bakin babban daraktan yada labaran shi Mista Gabriel Otobong yace mutane akalla magoya bayan Atiku sama da 800,000 a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya.

Da dumin sa: Atiku Abubakar ya rasa magoya baya sama da 800,000 kudancin Najeriya

Da dumin sa: Atiku Abubakar ya rasa magoya baya sama da 800,000 kudancin Najeriya
Source: Twitter

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC tayi karin haske game da labarin maganar cire Mukaddashin shugaban hukumar Ibrahim Magu da ake ta yadawa a kafafen sadarwar zamani.

Hukumar a ta bakin jami'in hulda da jama'ar ta, Mista Tony Orilade da yake bayar da karin haske game da lamarin yayin zantawar sa da kamfanin dillacin labarai yace maganar ba tada tushe ma balle makama don kuwa kanzon kurege ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel