Dalilin da yasa Dino Melaye ke dandana kudar sa hannun gwamnatin Buhari - Saraki

Dalilin da yasa Dino Melaye ke dandana kudar sa hannun gwamnatin Buhari - Saraki

Shugaban majalisar dattawan Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Bukola Saraki ya bayyana cewa dalilin da yasa gwamnatin Shugaba Buhari ke ganawa Sanata Dino Melaye azaba shine don ta muzgunawa jam'iyyar PDP da kuma majalisa.

Sanata Saraki ya yi wannan ikirarin ne a yayin da yake jawabi ga dumbin magoya bayan jam'iyyar ta PDP lokacin gangamin yakin neman zaben dan takarar shugabancin kasar Najeriya a tutar PDP Alhaji Atiku Abubakar a garin Jos.

Dalilin da yasa Dino Melaye ke dandana kudar sa hannun gwamnatin Buhari - Saraki

Dalilin da yasa Dino Melaye ke dandana kudar sa hannun gwamnatin Buhari - Saraki
Source: UGC

KU KARANTA: EFCC tayi karin haske game da inda maganar tura Magu karatu ta tsaya

Legit.ng Hausa ta kuma samu cewa Saraki din dake zaman shugaban kwamitin gangamin yakin neman zaben Atiku Abubakar din ya kuma bayyana cewa hakan da ake yi masu ba zai taba sa gwuiwoyin su sanyi ba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a 'yan kwanakin nan Sanata Dino Melaye ya sha takaddama da jami'an tsaron kasar nan da suka hada da 'yan sanda da kuma 'yan sandan farin kaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel