Yanzu Yanzu: An sauya wa kwamishinan yan sandan Lagas, Imohimi Edgal wajen aiki

Yanzu Yanzu: An sauya wa kwamishinan yan sandan Lagas, Imohimi Edgal wajen aiki

- Hukumar yan sanda ta sauya wa kwamishinan yan sandan jihar Lagas wajen aiki

- An mayar da Mista Edgal zuwa hedkwatar rundunar da ke Abuja a matsayin kwamishinan yan sandan da ke kula da sashin bama-bamai

- Mista Kayosr Egbetokun ne zai maye gurbin Edgal a matsayin mukaddashin kwamishinan yan sanda a jihar

Hukumar yan sandan Najeriya ta sauya wa kwamishinan yan sanda jihar Lagas, Mista Imohimi Edgal, wajen aiki, Channels Tv ta ruwaito.

An mayar da Mista Edgal zuwa hedkwatar rundunar da ke Abuja a matsayin kwamishinan yan sandan da ke kula da sashin abubuwan fashewa, wata majiya ta bayyana hakan a ranar Lahad, 1 ga watan Janairu.

Yanzu Yanzu: An sauya wa kwamishinan yan sandan Lagas, Imohimi Edgal wajen aiki

Yanzu Yanzu: An sauya wa kwamishinan yan sandan Lagas, Imohimi Edgal wajen aiki
Source: Depositphotos

Hukumomin yan sandan ta kuma bukaci Mista Kayosr Egbetokun da ya ci gaba daga inda Mista Edgal ya tsaya a matsayin mukaddashin kwamishinan yan sanda a jihar.

A watan Agusta 2017, Legit.ng ta rahoto cewa IGP, Ibrahim Idris, ya nada Imohimi Edgal a matsayin sabon kwamishinan yan sandan jihar Lagas, biyo bayan Karin girma da Edgal ya samu daga hukumar yan sandan kasar.

KU KARANTA KUMA: Da dumin sa: Hukumar EFCC tayi karin haske game da labarin maganar tsige Magu

A cewar rahoton, Edgal ya kasance tsohon mataimakin kwamishinan yan sanda da ke kyla da ayyuka, a jihar Lagas.

An tattaro cewa ya taimaka wajen kawo karshen ayyukan yan kngiyar asirin nan ta Badoo da yan bindiga dake aiwatar da aikin sace-sacen mutane a cikin Ikorodu da garuruwan kewaye.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel