Da dumin sa: Hukumar EFCC tayi karin haske game da labarin maganar tsige Magu

Da dumin sa: Hukumar EFCC tayi karin haske game da labarin maganar tsige Magu

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC tayi karin haske game da labarin maganar cire Mukaddashin shugaban hukumar Ibrahim Magu da ake ta yadawa a kafafen sadarwar zamani.

Hukumar a ta bakin jami'in hulda da jama'ar ta, Mista Tony Orilade da yake bayar da karin haske game da lamarin yayin zantawar sa da kamfanin dillacin labarai yace maganar ba tada tushe ma balle makama don kuwa kanzon kurege ce.

Da dumin sa: Hukumar EFCC tayi karin haske game da labarin maganar tsige Magu

Da dumin sa: Hukumar EFCC tayi karin haske game da labarin maganar tsige Magu
Source: Facebook

KU KARANTA: Dan majalisar wakilai daga APC ya koma PDP

Legit.ng Hausa ta samu cewa Mista Tony Orilade ya kara da cewa a yanzu shi Mista Magu ba abunda ke gaban sa ma sai karin jajircewa da yayi domin ganin ya kakkabe kasar daga dukkan cin hanci da rashawa.

A baya dai mai karatu zai iya tuna cewa an yi ta yamadidi da labarin cewa Mista Ibrahim Magu za'a tura shi karatu domin ya sauka daga kan mukamin sa a dora wani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel