Goyon bayan Buhari da kake yi ya saba ma ra’ayin yan Igbo – Atiku ga Obiano

Goyon bayan Buhari da kake yi ya saba ma ra’ayin yan Igbo – Atiku ga Obiano

- Dan takarar PDP, Atiku Abubakar ya bukaci Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra da ya anye daga goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari

- A wata sanarwa da ya saki kwanan nan, Atiku yayi ikirarin cewa kamfen din da Gwamna Obiano ke yiwa shugaba Buhari ya saba ma ra’ayin yan Igbo

- Atiku yayi zarin cewa shugaban kasa na ci gaba da ware kudu maso gabas daga aikin hada hanyoyi ta filin jirgin kasa da ake gudanarwa a fadin kasa, rashin tsaro da kuma hana du mukaman siyasa

Dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ta hannun Darakta Janar na kungiyar kamfen din Atiku-Obi , Dr. Harry Oranezi ya gargadi Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, da ya daina yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kamfen.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa gargadin na zuwa ne bayan wani furuci da aka ce Obiano yayi inda ya bayyana cewa Buhari yayi kokari a yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudu kan dawo da aiki da yayi a gadar Niger na biyu.

Goyon bayan Buhari da kake yi ya saba ma ra’ayin yan Igbo – Atiku ga Obiano

Goyon bayan Buhari da kake yi ya saba ma ra’ayin yan Igbo – Atiku ga Obiano
Source: UGC

An kuma tattaro cewa gwamnan ya yaba ma Buhari akan kammala aikin ginin Zik a Onitsha, wanda aka fi sani da wajen Zik, an bayar da aikin shekaru 22 da suka gabata, amma duk gwamnatocin da suka biyo baya sai suka yasar da shi.

Amma Atiku yace goyon bayan da Obiano ke nuna ma Buhari ya sabama ra’ayin yan Igbo

Yace duk wani hada kai, da shiri da wasu za su yi don su yaudari yan kabilar Igbo ta hanyar shirya zance ba zai yi tasiri ba akansu ko kadan.

KU KARANTA KUMA: Murna a APC yayinda dan takarar gwamna na PDP ya sauya sheka a Jigawa

Atiku yayi zarin cewa shugaban kasa na ci gaba da ware kudu maso gabas daga aikin hada hanyoyi ta filin jirgin kasa da ake gudanarwa a fadin kasa, rashin tsaro da kuma hana du mukaman siyasa

A wani lamari na daban, mun ji cewa Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus a ranar Asabar ya yi zargin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyya mai mulki ta APC, sun fito ne haikan domin tarwatsa kasar.

Da yake zayyana hanyoyin da shugaban kasa Buhari da APC suka dauka don tarwatsa katsar, Secondus, a yayin da yake jawabi a taron yakin zaben PDP a Jos, jihar Filato, ya ce: "Buhari da APC na son tarwatsa Najeriya. Sun fara ne da 'yan siyasa daga baya kuma suka koma kan 'yan majalisu. Kuna sane da cewa akwai lokuta da dama da akayi yunkurin juyin mulki a majalisar tarayya, wanda basu samu nasara ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel