Idan na samu mulki, ba zan tirke Mata a cikin daki ba – inji Atiku Abubakar

Idan na samu mulki, ba zan tirke Mata a cikin daki ba – inji Atiku Abubakar

Labari ya iso gare mu cewa ‘dan takarar PDP na shugaban kasa a zaben da za ayi a Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana abin da zai faru da matan kasar nan idan har ya samu shugabancin kasar a bana.

Idan na samu mulki, ba zan tirke Mata a cikin daki ba – inji Atiku Abubakar

Mata za su samu 35% na mukaman Atiku idan ya kafa Gwamnati
Source: UGC

Atiku Abubakar yayi alkawari cewa, mata za su dama kwarai a gwamnatin sa idan har su kayi kokari wajen ganin PDP ta kai ga ci a zaben 2019. Atiku ya bayyana wannan ne lokacin da ya gana da wasu mata a Garin Abuja.

‘Dan takarar na jam’iyyar PDP yana cigaba da kokarin ganin ya samu goyon bayan al’umma a Najeriya, inda ta kai ya zanta da wasu mata da ke da ra’ayin kan harkar siyasa a babban birnin tarayya a shekaran jiya Ranar Juma’a.

KU KARANTA: 2019 : Ba na tafiya da masu kashi a jikin su - inji Atiku Abubakar

Atiku wanda ya shafe fiye da shekaru 30 yana neman shugabanci a matakai daban-daban, yace Mata sun fi kowa jajircewa a harkar siyasa. ‘Dan takarar yace Mata sun fi maza himma da azama wajen marawa ‘yan takara baya.

Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar, yayi alkawarin cewa muddin yayi nasarar zama shugaban kasa, ba zai juyawa mata baya ba. ‘Dan takaran yake cewa ko a wajen layin zabe, adadin mata ya kan ribanya maza sau 3.

A cewar ‘dan takarar, ba zai bar mata su yi ta zama a dakunan gidajen su idan ya zama shugaban kasa ba. Atiku ya nuna cewa da iyalin sa yake yawo domin Duniya ta fahimci cewa mata za su tashi da kashi 35% na mukaman da zai raba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel