Saidu Kumo da ya koma goyon bayan Buhari bai cikin jagororin mu - PPCO

Saidu Kumo da ya koma goyon bayan Buhari bai cikin jagororin mu - PPCO

Kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar na PPCO ya fito yayi magana game da rade-radin da ke yawo na cewa wasu manyan jagorori wajen kamfen din PDP sun sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC.

Saidu Kumo da ya koma goyon bayan Buhari bai cikin jagororin mu - PPCO

Atiku yace bai san da zaman Sanata Saidu Koma a tafiyar PDP ba
Source: Facebook

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa babu wani daga cikin manyan masu taya ta yakin neman zaben shugaban kasa a zaben da za ayi da su ka koma jam’iyyar APC mai mulki a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

PDCO tayi wannan jawabi ne ta bakin Mista Kola Ologbondiyan, wanda shi ne Darektan yada labarai da cikin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar na PDP. Ologbondiyan yace Atiku bai da wani Darektan neman takara.

A makon nan ne aka yi ta rade-radin cewa Saidu Kumo wanda ake da'awar shi ne babban Darektan da ke taya Atiku kamfe a Arewa maso Gabas ya saki layin PDP inda yayi alkawarin taya shugaba Buhari kamfe a zaben bana.

KU KARANTA: Babban Sanatan PDP ya kauracewa kamfen din Atiku gaf da zaben 2019

Jam’iyyar PDP tayi cikakken bayani tana mai cewa babu wanda ya nada Said Kumo cikin tafiyar yakin neman zaben Atiku domin kuwa 'dan takarar na ta ba ya tafiya da wadanda ake zargi da laifin satar kudin gwamnati a kwamitin sa.

Kola Ologbondiyan yace wanda ya ke da alhakin jan ragamar yi wa Atiku kamfe a 2019 a yankin Arewa maso Gabashin kasar shi ne gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo. PDP tace sam ba ta nada kowa a matsayin Darektan ta ba.

Kwamitin na PPCO tayi kira ga mutane su yi watsi da labaran da ke fitowa daga kwamitin neman tazarcen shugaba Muhammadu Buhari, a cewar kwamitin zaben na PDP, ba yau na kusa da shugaban kasar su ka fara sharba karya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel