Suna son a tsige Onnoghen domin samun damar yin magudin zabe - Clark

Suna son a tsige Onnoghen domin samun damar yin magudin zabe - Clark

- Chief Edwin Clark ya bayyana kaduwarsa kan yunkurin da ake yi na maka babban jojin Nigeria, mai shari'a Walter Onnoghen

- Clark ya ce ana son tsige babban jojin ne kawai don nada wani da zai taimaka wajen tabka magudi a zaben 2019 da ke karatowa

- A ranar Litinin ne ake sa ran za a gurfanar da Walter Onneghen a gaban kotu, bisa zarginsa da kin bayyana gaskiyar kadarorin da ya mallaka

Jagoran kungiyar Pan Niger Delta (PANDEF) da kuma kungiyar shiyyar Kudu maso Kudu, Chief Edwin Clark ya bayyana kaduwarsa kan yunkurin da ake yi na maka babban jojin Nigeria, mai shari'a Walter Onnoghen, bisa zarginsa da kin bayyana gaskiyar kadarorin da ya mallaka.

Ya ce wannan yunkurin abun daga hankali ne, musamman la'akari da cewa babban jojin yana gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.

Ya bayyanawa jaridar Daily Trust ta ranar Lahadi cewa kungiyar ba zata lamunci wannan cin fuskar da ake yunkurin yiwa babba jojin ba.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Rundunar soji ta gano yadda Boko Haram ke samun abinci da makamai

Suna son a tsige Onnoghen domin samun damar yin magudin zabe - Clark

Suna son a tsige Onnoghen domin samun damar yin magudin zabe - Clark
Source: Depositphotos

Da yake jawabi da wakilin jaridar ta wayar tarho a daren ranar Asabar, Clark ya ce: "Labarin gurfanar da babban jojin Nigeria, mai shari'a Walter Onnoghen a gaban kotun ladabtarwa CCT a ranar litinin, ya zo mana cikin tashin hankali, saboda babu wata hujja da zata nuna cewa wannan mutumin ya aikata wani laifi wajen gudanar da aikinsa.

"Babu wata hujja da za a nuna akan zarginsa da rasawa; kawai dai suna so ne su tabka magudin zabe, suna son su cire shi su kaw wani wanda zai zama karen farautarsu, idan ba hakan ba to kuwa babu dalilin ci masa fuska haka," a cewar Clark.

Chief Clark ya ce: "Jiya, mukaddashin darakta janar na hukumar tsaron cikin gida DSS, Mathew Seyeifa aka tsige, aka nada wani wanda tuni yayi ritaya a matsayin sabon darakta janar na DSS."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel