Da duminsa: Rundunar soji ta gano yadda Boko Haram ke samun abinci da makamai

Da duminsa: Rundunar soji ta gano yadda Boko Haram ke samun abinci da makamai

- Rundunar soji, a ranar Lahadi ta ce ta gano hanyoyin da mayakan Boko Haram ke samun kayayyakin da suke amfani da su

- Bulama Biu, mukaddashin babban jami'in da ke jagorantar rundunar soji ta 7 ya bayyana cewa sun gano cewa akwai masu gudanar da kasuwanci a madadin mayakan BH

Mr Biu ya ce sun haramta safarar itace da gawayin ne na dan wani lokaci don gudanar da bincike kan masu safarar da nufin gano bakin zaren lamarin

Rundunar soji, a ranar Lahadi ta ce ta gano hanyoyin da mayakan Boko Haram ke samun kayayyakin da suke amfani da su, inda suke amfani da sojin gona kamar masu sara da sayar da gawayi a jihar Borno.

Bulama Biu, mukaddashin babban jami'in da ke jagorantar rundunar soji ta 7, ya bayyana hakan a wata zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Maiduguri.

Mr Biu, wanda kuma birgediya janar ne a rundunar soji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi kan dalilin rundunar na haramta safarar itatuwa da gawayi a jihar Borno.

KARANTA WANNAN: Gurfanar da babban joji na kasa a kotu: Gwamnonin Kudu maso Kudu zasu gana a Abuja

Da duminsa: Rundunar soji ta gano yadda Boko Haram ke samun abinci da makamai

Da duminsa: Rundunar soji ta gano yadda Boko Haram ke samun abinci da makamai
Source: Twitter

Ya bayyana cewa sun samu rahotanni daa majiya mai tushe na yadda wasu diloli a Maiduguri ke fakewa da safarar itace da gawayi wajen kaiwa mayakan Boko Haram kayayyakin da suke amfani da su.

"Wasu daga cikin 'yan aiken mayakan Boko Haram ne, suna boye abinci, magunguna, fetur da sauran kayayyaki a karkashin motocinsu, inda suke kaiwa mayakan. Haka zalika mun gano cewa wasu daga cikinsu na gudanar da kasuwanci a madadin mayakan.

"Sukan kutsa su shiga cikin kungurmin dajin inda wani mahaluki bai isa ya je ba; da sunan zasu sari itatuwa, su kona, domin samar da gawayi. Sai dai ba hakan bane manufarsu, suna zuwa ne don haduwa da mayakan Boko Haram, su karbi sako daga wajensu, ko kuma su basu aiken da aka yi masu," a cewarsa.

Mr Biu ya bayyana cewa sun haramta safarar itace da gawayin ne na dan wani lokaci don gudanar da bincike kan masu safarar da nufin gano bakin zaren lamarin, ba wai sunyi hakan don kuntatawa masu sana'ar sayar da itace ko gawayi ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel