Haramta shan barasa a jihar Kano ba ya cin karo da kundin tsarin mulkin Najeriya - Shugaban Hukumar Hisbah

Haramta shan barasa a jihar Kano ba ya cin karo da kundin tsarin mulkin Najeriya - Shugaban Hukumar Hisbah

A kwana-kwanan nan mun kawo muku rahoton yadda hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta tarwatsa wasu kwalabai na barasa makire cikin motoci 30 ma su dakon kaya. Wannan lamari ya janyo cecekuce tare da ci gaba na barin baya da kura.

Shugaban hukumar Hisbah na jihar, Dakta Abba Sufi, shine ya labarta wannan lamari yayin amsa tambayoyin manema labarai da cewa, gwamnatin jihar Kano ta dauki wannan salo na harama fatauci da ta'ammali da barasa tun a shekarar 2004 da ta gabata.

Dakta Sufi yayi furucin hakan ne a yayin mayar da martani dangane da yadda lamarin haramta barasa a jihar Kano a halin yanzu yake ci gaba da barin baya da kura gami da fuskantar cecekuce musamman a mahanga ta kundin tsarin mulkin Najeriya.

Gwamnan jihar Kano; Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jihar Kano; Abdullahi Umar Ganduje
Source: Depositphotos

Wani fitaccen lauya mazaunin jihar Legas mai kare hakkin bil Adama, Mista Ebu-Olu Adegboruwa, ya ce tsarin dokokin gwamnatin jihar Kano na haramta fatauci da ta'ammali da barasa na cin karo gami da sabawa kundin tsarin mulki na kasar nan.

Mista Adegboruwa ya hikaito yadda sashe na goma cikin kundin tsarin mulkin Najeriya ya haramtawa kowace jiha riko da kowane nau'i na addini da a halin yanzu jihar Kano ke ribatar shari'ar addinin musulunci wajen haramtawa al'umma 'yancin su na rayuwa.

KARANTA KUMA: Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PPC ya sha alwashin lallasa Buhari da Atiku a zaben 2019

Cikin zayyana damuwar sa Mista Adegboruwa ya ce, tsantsar siyasa ta neman suna da samun shiga wurin al'umma ya sanya jihar Kano ta zartar da wannan danyen hukunci yayin da babban zabe ya gabato.

A yayin ci gaba da raddi gami da mayar da martani, shugaban hukumar Hisban ya ce, gwamnatin jihar Kano na dama a bisa tanadi na kundin tsarin mulkin Najeriya ta shimfida dokoki daidai da kare martabar dabi'un al'ummar ta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel