Ya kamata Yarabawa su zabi Buhari domin karrama mahaifina - Jamiu Abiola

Ya kamata Yarabawa su zabi Buhari domin karrama mahaifina - Jamiu Abiola

- Jamiu Abiola ya bukaci daukacin al'ummar Yarabawa da su fito kwansu da kwarkwatarsu don kad'a kuri'arsu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019

- Jamiu, wanda a cewarsa, hakan ne zai karrama mahaifinsa ya kuma ce yana da tabbacin cewa Yarabawa ba zasu juyawa mahaifinsa baya ba duk da ya mutu

- Jamiu ya ce ko kadan bai kamata a kira Buhari da mai nuna kabilanci ba, inda ya kara da cewa, karrama mahaifinsa da shugaban kasar yayi ta tabbatar da hakan

Yaron Chief Moshood Abiola, wanda ya lashe zaben shugaban kasa a ranar 12 ga watan Yuni, 1993, wanda aka rushe, Jamiu a ranar Asabar ya bukaci daukacin al'ummar Yarabawa da su fito kwansu da kwarkwatarsu don kad'a kuri'arsu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda a cewarsa, hakan ne zai karrama mahaifinsa.

Jamiu, wanda yana daga cikin mambobin hukumomin gudanarwar kungiyar mata da matasa ta yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu, ya bayyana Buhari a matsayin shugaban da baya nuna banbancin yare ko addini a shugabancinsa.

Da yake jawabi ga manema labarai a Legas, Jamiu ya ce ko kadan bai kamata a kira Buhari da mai nuna wariyar kabila ba, inda ya kara da cewa, idan da ace Buhari na nuna wariyar kabila da kuwa bai karrama mahaifinsa ba duk da cewa anyi shekaru 25 da rushe zabensa.

KARANTA WANNAN: Buhari bai umurci CJN Onneghen yayi murabus ba - Ojudu

Ya kamata Yarabawa su zabi Buhari domin karrama mahaifina - Jamiu Abiola

Ya kamata Yarabawa su zabi Buhari domin karrama mahaifina - Jamiu Abiola
Source: UGC

Ya bukaci daukacin al'ummar Yarabawa da su sake zabar Buhari a ranar 16 ga watan Fabreru, don kar su baiwa mahaifinsa Abiola da matarsa Kudirat kunya, wadanda suke kwance a cikin kabarinsu.

Ya ce: "Ya kamata mutane su gane cewa duk mutumin da zai karrama wata nasara da wani mutumi ya samu, kuma daga wata kabila, to kuwa bai kyautu a kirashi mai nuna kabilanci ba. Idan da har mai nuna kabilanci ne, da bai karrama ranar nasarar M.K.O Abiola ba.

"Buhari ya ce a cikin wata wasika cewar 12 ga watan Yuni tafi daraja akan ranar 'yancin kasar, don haka 'yan Nigeria su fahimci hakan, kuma ina da yakinin cewa Yarabawan da na sani ba zasu juyawa Chief M.K.O Abiola baya ba duk da yana kwance a cikin kabarinsa."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel