Manyan Lauyoyi za su ba CJN Walter Onnoghen kariya a gaban kuliyar CCT

Manyan Lauyoyi za su ba CJN Walter Onnoghen kariya a gaban kuliyar CCT

Mun ji cewa akalla wasu manyan Lauyoyi 150 da su ka rika a harkar shari’a ne za su tsayawa Alkalin Alkalan Najeriya, Walter Samuel Nkanu Onnoghen, da ake zargi da rashin gaskiya a gaban kotun CCT.

Manyan Lauyoyi za su ba CJN Walter Onnoghen kariya a gaban kuliyar CCT

Kotun CCT za ta binciki Alkalin Alkalan na Najeriya gobe
Source: Facebook

Sama da Lauyoyi 100 na Najeriya wadanda su ka kai mataki na SAN ne su ka da shirin kare babban Alkalin kasar daga zargin da ke kan sa na kin bayyanawa hukuma kadarorin sa. Wani Lauya, Sebastine Hon ya bayyana wannan.

A jiya Asabar ne, Barisa Sebastine Hon SAN, wanda kwararre ne a kan dokar kasa, ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewa akalla su 150 za su kare babban Alkali watau Walter Onnoghen ba tare da kuma an biya su ko da sisin kobo ba.

KU KARANTA: Gwamnonin kudu sun kira taron gaggawa bayan sun ji za a gurfanar da CJN

Hon ya bayyana cewa maka babban Alkalin kasar da aka yi a gaban kotu, wani yunkuri ne na hana bangaren shari’a na Najeriya ta-cewa. Babban Lauyan yace akwai burbushin siyasa a wannan mataki gwamnati da gwamnati ta dauka.

Lauyan ya yarda cewa Alkalin Alkalan bai wuce kotu ta bincike sa ba, sai dai yana ganin akwai alamar tambaya a lamarin. Son SAN ya kuma fadawa babban Alkalin cewa yayi watsi da kiran da ake yi masa na sauka daga kujerar sa.

Lauyan yayi tir da jawabin da shugaban kasa ya fitar na cewa Alkalin Alkalan ya sauka daga kan kujerar sa. Sebastine Hon yace babu abin da zai sa Mai girma mai shari’a Onnoghen yayi murabus ba tare da an kama sa da wani laifi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel