Mataimakin Shugaban Majalisa Ekweremadu yayi watsi da yakin neman zaben Atiku

Mataimakin Shugaban Majalisa Ekweremadu yayi watsi da yakin neman zaben Atiku

- Da alamu Sanata Ekwerenadu yayi watsi da yakin neman zaben Atiku Abubakar

- Babban Sanatan Kasar ba ya cikin wadanda PDP ta ba wani aiki a zaben na 2019

- Wani na-kusa da Mataimakin Shugaban Majalisar yace ba abin tada hankali bane

Mataimakin Shugaban Majalisa Ekweremadu yayi watsi da yakin neman zaben Atiku

Ba a ganin Sanata Ekweremadu a cikin jirgin yakin zaben Atiku
Source: Depositphotos

Dazu nan mu ka ji labari cewa mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekwerenadu, yana nesanta kan sa daga yakin neman zaben PDP. Sanatan ya kauracewa kamfen din da Atiku Abubakar yake yi.

Wata jaridar kasar nan ta rahoto cewa Ike Ekweremadu yana cigaba da yin baya-baya daga harkar takarar Atiku Abubakar a PDP. Masu hangen nesa a harkar siyasa sun bayyana cewa hakan ya kawowa jam’iyyar adawar nakasu.

Wani wanda ke tare da Ekweremadu ya musanya wannan rahoto inda ya bayyana cewa PDP ba ta ba Sanatan wani aiki na musamman a cikin tafiyar yakin neman zaben na Atiku ba. Tace wannan ya sa aka ga ba ya ruwa-da-tsaki.

KU KARANTA: Gwamnonin PDP su na yi wa Buhari aiki a maimakon Atiku a 2019

Hadimin na Sanatan yace jam’iyyar PDP ba ta kyauta da ta ki ba Ike Ekweremadu wannan mukami na musamman a cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar ba. Saraki shi ne Darektan yakin neman zaben Atiku a 2019.

Manyan mukarraban Sanatan sun tabbatar da cewa Ekweremadu yana cikin wadanda su ka tafi har Gombe domin taya Atiku kamfe. Yanzu haka dai a cewar su, Sanatan ya fi karkatar ne a yankin san a Kudu maso Gabashin kasar.

‘Yan hannun-daman Sanatan sun ce za a ga Ekweremadu a wajen kamfen din Atiku idan PDP ta leko Kudancin kasar domin kuwa ba dole bane sai 'dan majalisar ya rika bin kwamitin kamfen din zuwa Sokoto da irin su Bauchi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel