Tashar Baro za ta soma aiki kwanan nan inji Farfesa Osinbajo

Tashar Baro za ta soma aiki kwanan nan inji Farfesa Osinbajo

Mataimakin shugaan kasar Najeriya, Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kaddamar da tashar ruwan nan na Baro da ke cikin jihar Neja a Arewacin kasar.

Tashar Baro za ta soma aiki kwanan nan inji Farfesa Osinbajo

Yemi Osinbajo yace ta gama karewa jam’iyyar PDP a Najeriya
Source: Facebook

Yemi Osinbajo ya bada wannan tabbaci ne a wajen wani taro na yakin neman zaben APC da aka shirya a babban garin Minna da ke cikin jihar Neja. Osinbajo yace wannan gagarumin aiki yana cikin manyan kudirorin gwamnatin Buhari.

Farfesa Osinbajo, yake cewa gwamntocin PDP da aka yi a baya, sun yi watsi da wannan aiki, inda su ka maida kwangilar tashar hanyar sace dukiyar jama’a. Yanzu dai kusan an kammala aikin wannan tasha kuma ana shirin bude ta.

KU KARANTA: Ministan Buhari ya bayyana irin mawuyacin hali da PDP ke ciki

A dalilin haka ne mataimakin shugaban kasar yayi kira ga mutanen Neja su bizne PDP a zaben da za ayi a bana. Osinbajo yace babu abin kirkin da PDP za ta iya yi idan ta samu mulki, don haka ya nemi a jefa ta a cikin makabartar siyasa.

Shi ma babban jigon APC, Rotimi Amaechi yayi irin wannan kira ga jama’a da su yi watsi da kiran da jam’iyyar PDP ta ke yi na a zabe ta a Najeriya. Amaechi yace PDP na neman dawowa mulki ne domin cigaba da satar kudin kasa.

A jihar Minna, inda jam’iyyar APC ta shiryawa Gwamna Abubakar Sani Bello kamfe domin ganin ya zarce kan kujerar sa, an karbi wasu tsofaffin ‘yan PDP da su ka sauya sheka zuwa APC mai mulki kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel