Kungiyar EU ta aiko Jakadun ta domin kula da zaben da za ayi a Najeriya

Kungiyar EU ta aiko Jakadun ta domin kula da zaben da za ayi a Najeriya

Mun samu labari cewa kungiyar kasashen nahiyar Turai na EU ta bayyana cewa ta soma turo Jakadun ta na musamman zuwa Najeriya domin lura da babban zaben da za ayi a kasar a shekarar bana.

Kungiyar EU ta aiko Jakadun ta domin kula da zaben da za ayi a Najeriya

Turai ta soma turo Jakadun ta na musamman domin zaben Najeriya
Source: Depositphotos

A Ranar juma’ar nan ne Kungiyar EU ta fitar da jawabi ta bakin mataimakin shugaban ta kuma babban mai lura da sha’anin kasashen ketare da kuma sha’anin tsaro, Federica Mogherini, yace sun fara shiryawa zaben Najeriya.

Mogherini ya tabbatar da cewa babbar jami’ar su watau Maria Arena, ita ce za ta jagoranci kwamitin EU COM da zai sa idanu a babban zaben da za ayi Najeriya. Misis Arena, mutumiyar kasar Beljika ce asalin ta da ke aiki da kungiyar EU.

A jawabin da F. Mogherini ya fitar a Ranar Juma'a, ya nuna cewa zaben Najeriya yana da tasiri da kuma muhimmanci ga kasahen na Turai saboda irin girman Najeriya a Nahiyar. Kungiyar tace za tayi kokarin ganin an yi zaben kwarai.

KU KARANTA: 2019: Jigon PDP ya sauya sheka daga zuwa APC a Najeriya

A bangaren ita kuma M. Arena wanda aka nada ta jagoranci Tawaga ta musamman zuwa Najeriya, ta nuna shirin ta na ganin Damukaradiyya ya nuna halin sa a zaben da za ayi. Tun a farkon shekarar nan ne Tawagar ta EU ta iso Najeriya.

Hukumar zabe na kasa a Najeriya watau INEC ce ta gayyaci kasashen na Turai da su halarci zaben da za ayi a bana daga tsakiyar watan gobe zuwa farkon Watan Maris. Tun 1999 dai ake yin haka domin tabbatar da sahihancin zaben kasar.

Jakadun na Nahiyar Turai za su zagaye kasar nan a lokacin babban zaben, kuma za su tsaya na kusan watanni 2 har sai zuwa lokacin da aka tabbatar da kammala zaben shugaban kasa da gwamnoni da sauran masu neman takarar kujeru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel