Ministan Buhari ya bayyana irin mawuyacin hali da PDP ke ciki

Ministan Buhari ya bayyana irin mawuyacin hali da PDP ke ciki

- A jiya, Asabar, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin neman zabensa na yankin arewa maso gabas a jihar Bauchi

- Gwamnoni, ministoci, da manyan jami'an gwamnati da shugabannin jam'iyyar APC sun halarci taron yakin neman zaben

- Jama'ar jihar Bauchi sun yi tururuwar fitowa domin nuna goyon bayansu ga shugaba Buhari da jam'iyyar APC

Rotimi Amaechi, sarkin yakin neman sake zaben shugaba Buhari a karo na biyu, ya bayyana cewar jam'iyyar PDP na cikin halin yunwa da fatara.

Amaechi, mai rike da mukamin ministan sufuri, ya bayyana hakan ne a yau, Asabar, a wurin taron kamfen din Buhari da aka yi a jihar Bauchi.

A cewar sa, "basu da kudi, sun tsiyace sannan ga yunwa da suke fama da ita, shi yasa suke son dawowa gwamnati domin domin su sake tafka sata.

Ministan Buhari ya bayyana irin mawuyacin hali da PDP ke ciki

Amaechi da Buhari
Source: Twitter

"Saboda sun tsiyace, sun shiga neman duk hanyar da zasu bi domin samun damar sake yin sata, shi yasa suke cewa ana yunwa.

"Sun manta cewar sun saci dalar Amurka $2bn domin su ci zaben shekarar 2015 amma duk da haka muka kayar dasu."

DUBA WANNAN: Kamfen: Dandazon masoya da magoya bayan Atiku a jihar Filato, hotuna

Sannan ya cigaba da cewa, "muna gefe, muna kallonsu suna fadawa jama'a cewar ana yunwa bayan sun sace masu kudi.

"Muna tabbatar da maku da cewar bamu ci amanar ku ba kuma ba zamu taba cin amanar ku ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel