Kotun da'ar ma'aikata ta kafa kwamitin tuhumar alkalin alkalai

Kotun da'ar ma'aikata ta kafa kwamitin tuhumar alkalin alkalai

Kotun da'ar ma'aikata CCT ta kafa kwamiti da za ta yiwa alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen shari'a bisa zarginsa da akeyi da karya wajen bayyana kadarorinsa.

A ranar Asabar ne kotun da sanar da cewa an shigar da kara a kan Mr Onnoghen kuma za a gurfanar da shi ranar Litinin 14 ga watan Janairun 2019.

Wata kungiyar kungiya mai rajin ci gaban al'umma da yaki da rashawa ne ta shigar da karar a kan alkalin alkalan.

Kotun da'ar ma'aikata ta kafa kwamitin tuhumar alkalin alkalai

Kotun da'ar ma'aikata ta kafa kwamitin tuhumar alkalin alkalai
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Legas: An kama manyan 'yan kasuwa dake daukar nauyin 'yan bindigar Zamfara

A sanarwar da ta fitar, kotun da'ar ma'aikatan ta ce "za a fara sauraron shari'ar ne saboda karar da shugaban kotun da'ar ma'aikatan ya shigar da jiya domin gurfanar da alkalin alkalan Najeriya bisa tuhumarsa da aikata laifuka shida".

"An shigar da karar ne a jiya dauke da sa hannun wasu jami'an kotun da'ar ma'aikatar Musa Ibrahim (Esq) da Fatima Danjuma Ali (Esq) dauke da tuhume-tuhume guda shida masu alaka da rashin bayyana kadarori," inji sanarwar da kakakin CCT, Ibrahim Al-Hassan ya fitar.

Za a fara shari'ar ne a ranar Litinin 14 ga watan Janairu a hedkwatan kotun da ke Jabi Daki Biyu, Solomon Lar way, Abuja misalin karfe 10 na safiya karkashin jagorancin Justice Danladi Umar.

A wani baya, Legit.ng ta ruwaito muku cewar gwamnonin yankin Kudu maso Kudu sun kira taron gaggawa domin cimma matsaya a kan gurfanar da alkalin alkalan na kasa, Walter Onnoghen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel