Badakalar alkalin alkalai: Jam'iyyar PDP ta ce ta gano dubarar Shugaba buhari

Badakalar alkalin alkalai: Jam'iyyar PDP ta ce ta gano dubarar Shugaba buhari

Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa ta gano dubarar shugaba Buhari da gwamnatin tarayya akan maganar gurfanar da Alkalin-alkalai Mai shari'a Walter Onnoghen da za'ayi a kotun tabbatar da da'ar ma'aikata ranar Litinin mai zuwa.

Jam'iyyar ta PDP ta bakin mai magana da yawun ta Mista Kola Ologbondiyan da ke zaman kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya bayyana cewa gwamnatin ta yi hakan ne domin kawai ta hargitsa bangaren shari'a yayin da aka kusa yin zabe.

Badakalar alkalin alkalai: Jam'iyyar PDP ta ce ta gano dubarar Shugaba buhari

Badakalar alkalin alkalai: Jam'iyyar PDP ta ce ta gano dubarar Shugaba buhari
Source: Depositphotos

KU KARANTA: PDP ta kwashe jiga-jigan APC a Jigawa

Legit.ng Hausa ta samu cewa jam'iyyar ta PDP haka zalika ta bayyana rashin amincewar ta game da matakin na gurfanar da Alkalin alkalan Mai shari'a Walter Onnoghen da za'a yi ba.

Shi ma dai Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya ce duk wani uzuri da gwamnatin tarayya zata yi amfani da shi domin kawar da alkalin alkalai na kasa, Walter Onnoghen, daga ofis za a bashi wata ma'ana ta daban.

Dan takarar na wadannan kalamai ne a matsayin martani ga karar da hukumar da'ar ma'aikata (CCB) ta kai Onnoghen.

A yau, Asabar ne, shugaban sashen yada labarai na kotun da'ar ma'aikata (CCT), Ibraheem Al-Hassan, ya bayyana cewar a ranar Litinin ne za a gurfanar da Onnoghen a gaban kotusu.

Za a gurfanar da alkalin alakalan ne bayan wani rubutaccen korafi da aka yi a kansa.

Sai dai, a wani jawabi, Atiku ya ce duk wani yunkurin taba Onnoghen zai kara rura wutar zargin cewar Muhammadu Buhari na son yin raba shi da kujerar sa ne saboda zabe mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel