Zabe: 'Yan takarar gwamna hudu daga PDP sun dunkule sun koma APC a Arewa

Zabe: 'Yan takarar gwamna hudu daga PDP sun dunkule sun koma APC a Arewa

Tsaffin 'yan takarar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) guda hudu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare da magoya bayansa a jihar Neja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mataimakin Shugaban jam'iyyar na kasa reshen Kudu, Mr Adeniyi Adebayo ne ya tarbi sabbin mambobin da magoya bayansu a wurin taron kaddamar da yakin neman zaben gwamna a ranar Asabar a garin Minna.

Tsaffin 'yan takarar gwamnan sun hada da Mr Ahmed Ibeto, Alhaji Hanafi Sudan, Mr Ahmed Baka da Mr Umaru Ahmed wanda akafi sani da Dogon Koli.

Zabe: 'Yan takaran gwamna hudu daga PDP sun dunkule sun koma APC a Arewa

Zabe: 'Yan takaran gwamna hudu daga PDP sun dunkule sun koma APC a Arewa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 2019: Ku zabi Buhari, kungiyar Izala ta umurci 'ya'yanta

A yayin da ya ke jawabi a madadin sauran, Ibeto ya bawa jam'iyyar ta APC tabbacin za suyi aiki tukuru domin ganin jam'iyyar tayi nasara a babban zaben da ke tafe.

A wurin taron, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce ya yi imanin cewa jam'iyyar APC ne za tayi nasara a babban zaben da ke tafe.

"Ina son in fada muku cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dukufa wajen inganta rayuwan 'yan Najeriya. Layin dogo na Kano zuwa Legas yana daya daga cikin ayyukan da shugaban kasar ya yi domin saukaka wa al'umma tafiye-tafiye.

"Kammala aikin tashan jiragen ruwa na Baro alama ce da ke nuna gwamnatin nan ta al'umma ce," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel